✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kama Nnamdi Kanu ba daidai ba ne – Soyinka

Ya ce za a sami tashin-tashina a kasar nan muddin aka gano gaskiyar yadda aka kama shi.

Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya zargi Gwamnatin Tarayya kan kama jagoran ’yan awaren Biyafara na IPOB, Nnamdi Kanu.

Ya yi zargin ne a wata tattaunawarsa da Sashen Pidgin na BBC a ranar Litinin.

Ya ce za a sami tashin-tashina a kasar nan muddin aka gano gaskiyar yadda aka kama shi ta saba da abin da gwamnatin ke fada.

A cewar Soyinka, “Ba ni zan fada wa Shugaban Kasa me zai faru ba idan har aka gano gaskiyar yadda aka kama Kanu. Mutane na ta gutsiri tsoma a kai.

“Wasu na zargin Najeriya ta taka dokokin kasa da kasa, sannan shi kuma dabi’un shi kansa Kanun a can.

“An fuskanci kalaman kiyayya iri-iri daga Kanu, kuma wannan laifi ne wanda dokokin kasar ne kawai zasu yi hukunci a kai.

“Shin daidai ne a yi garkuwa da shi? Na san wasu zasu ce kama shi aka yi, amma da ni da kai mun san garkuwa da shi aka yi, wannan kuma ba daidai ba ne ko a Najeriya ko a kasashen ketare,” inji shi.

Farfesa Soyinka ya kuma ce kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da zalama da wutar cikin da ta yi amfani da su wajen kama Kanu a yaki da ’yan bindiga da kuma masu tayar da kayar baya.

Ya kuma ce, “Buhari ya ce zai yi wa ’yan IPOB magana da yaren da suka fi fahimta, abin da ya kamata ya fada kenan a lokacin da aka fara rikicin Boko Haram.

“Hatta ’yan Miyetti-Allah kamata ya yi ace an kama su tun ma kafin a ayyana IPOB a mastayin kungiyar ta’addanci.”

Dagan an sai ya bukaci gwamnatin da ta daina nuna yatsa ta yi abin da ya kamata.