Kama Nastura Ashir Sharif da ‘yan sanda suka yi ba karamin hatsari ba ne, inji Alhaji Bashir Othman Tofa, dan takarar shugaban kasa a shekarar 1993.
Alhaji Bashir Tofa ya yi gargadi ya fadi hakan ne a wani hoton bidiyo lokacin da yake tsokaci game da kama Nastura bayan zanga-zangar lumanar da ya jagoranta a Katsina.
Tsohon dan siyasar ya kuma bukaci a yi gaggawar sakin matashin domin kama shi da aka yi ka iya ka iya tunzura matasa su ta da kayar baya.
- Matsalar tsaro: An kama jarogran zanga-zangar da aka yi a Katsina
- Buhari ya ba ’yan Katsina hakuri kan matsalar ’yan bindiga
“Wani abin bakin ciki da ya faru a tsakanin jiya (Laraba) da yau (Alhamis) shi ne akwai samari wadanda suke goben tasu ce, gobe tasu ce.
“Suka tashi saboda rashin tsaro a kasar nan musamman a ksasashen nan na Arewa Maso Yamma, suka ce lallai lallai suna kiran hukuma ta tashi ta tabbatar cewa an samu tsaro a wadannan gurare da kuma Arewa Maso Gabas da kuma ko ina a kasar nan.
“Suka yi taron su lami lafiya suka gama, abin ban sha’awa da na gani shi kansa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, ni da kai na ban taba ganin kwamishinan ‘yan sanda mai hankali da hikima irin sa ba, ya bi su kuma ya yi magana kyakkyawa, kuma ya nuna ko da yake ba su da izini amma dai ya yarda sun yi, kuma ya ba su shawarwari su yi lami lafiya kuma suka yi lami lafiya”, inji shi.
‘Rashin dabara’
Ya kuma nuna takaicinsa da kama wasu daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zanagr bayan sun kammala.
“Wannan wacce irin kasa ce? Wato ba ma wanda ya isa ya yi magana? Ba wanda ya isa ya ce abu kaza ba daidai ba ne? Ko da zai yi haka cikin lumana?
“Wannan gaskiya ina ganin cewa ba karamin rashin dabara ba ne, ba karamin rashin hikima ba ne ga su wadanda suka kukkulla aka kama wadansu daga cikin samarin nan wadanda suke kokarin tabbatar da cewa yau din nan ta gyaru wadanda goben nan tasu ce, domin gobensu ta yi kyau amma tsofaffi sun taru sun kewaye sun kama su…
“Ina kira ga shi kansa shugaban kasa, ina kira ga shi kansa Sufeto Janar na ‘yan sanda, da Babban Darakta na DSS, lallai su zauna su yi amfani da hankalinsu, su yi amfani da kwakwalwarsu su zamo masu kishi, su zamo masu adalci, su zamo masu son cigaba su saki yaron nan”, inji shi.
‘Kada a tashi hankali’
A karshe Alhaji Bashir Tofa wanda daya ne daga cikin dattawan jihar Kano, ya yi kira ga shugabanni da gwamnoni da su zamo masu kishin jama’arsu, masu yi masu adalci.
“Na san ya kwana kuma duk mun bincika mun ji, kuma mun aika duk inda muka san za mu iya aikawa da shawarwarin da ya kamata mu aika.
“Da wannan nake kiran jama’a su yi kokari su saurara musamman ma samari da aka kama shugabansu….kada su yi wani abu na tashin hankali domin a ga me hukuma za ta yi kan wannan lamari.”
An kama Nastura Ashir Sahrif ne jim kadan bayan da ya jagoranci Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) suka yi zanga-zangar lumana a Katsina.