✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kama Gwanja: Dalilin rashin kai wa ’yan sanda umarnin kotu —Lauya

Dalili, a cewarsa, shi ne saboda kurewar lokaci, amma za su kai takardar a yau don a yi abin da ya dace.

Lauyan da ya jagoranci shigar da karar mawaki shahararren mawakin Hausa Ado Gwanja a kotu, Barista Badamasi Gandu, ya yi martani game da rashin kama mawakin.

Barista ya yi magana ne bayan jawabin da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta yi cewa ba ta sami umarnin ko kamun da ake cewa za ta yi wa shahararren mawaki Ado Gwanja ba.

Jawabin nasa na zuwa ne bayan kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa rundunar ba ta samu umarnin kotu ba.

A cewar Barista Gandu gaskiya ne ranar Talata bayan da kotun ta bayar da umarnin ba su samu sun kai takardar umarnin kamun Ado Gwanja ga ’yan sanda ba.

Dalili, a cewarsa, shi ne saboda kurewar lokaci, amma za su kai takardar a yau don a yi abin da ya dace.

Shi ma a nasa jawabin da ya wallafa a Facebook, Kiyawa ya kara da cewa da zarar sun samu umarnin kamun Ado Gwanja za su aiwatar ba tare da bata lokaci ba.

A ranar Litinin wata Babbar Kotu a Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta ba da umarnin kamo mawaƙi Ado Gwanja.

Kotun ta kuma haramta wa mawaƙin yin waƙa har zuwa lokacin da ’yan sanda za su kammala bincike a kansa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ta maka mawaƙin a kotu kan amfani da kalaman da ba su dace ba a waƙoƙinsa.