✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kalubalen zaben 2015

kasar nan na fuskantar kalubalen tsaro a yankin Arewa maso gabas, kuma matukar ba a yi zabe a Jihohin Barno d aYaobe da Adamawa ba,…

kasar nan na fuskantar kalubalen tsaro a yankin Arewa maso gabas, kuma matukar ba a yi zabe a Jihohin Barno d aYaobe da Adamawa ba, al’umma za ta fada cikin shakku, har ma a tabbatar da cewa gwamnati ba da gaske take ba.

Fargabata anan shi ne kar Najeriya ta sake komawa cikin halin da ta shiga a 1966. wato cewa wadansu su balle yanzu anayin zabe babu wadannan jahohi guda uku na yankin arewacin Najeriya ana yin zabe babu su du wani tattalin arziki da ake zubawa cikin jahohi su basa samunsu to dole abubuwa su tabarbare musamman.kasuwanci da ilimi da lafiya da kuma uwa Uba tsaro wato idan haka ta faru. Ba ma fata ta faru wadannan jahohin za su koma kamar ba a Najeriya suke ba, idan ya zamanto talawan da ke cikin wadanna jihohin guda uku. idan sukaga gwamnati bata shiga hurumunsu, za su iya hada kai da wadancan ‘Yan ta’addar na kungiyar boko haram to kaga idan gwamnati tayi sake nan gaba za su iya tashin wani yanki har su sa masa suna yankin Islama alhalin kamar yanda suke kiran wasu a kasar wanda abin ba haka yake ba ina ganin irin wadannan abubuwa da ace akwai gwamnati tsayayya duk da ba su bullo ba.
Wasu daga cikin manyan malamai masu nazarin siyasa da suka hada da Bawa Abdullahi Wase da Farfesa Bube da Alhaji. Abdulkarim dayyabu da sauransu suna fadar irin wadannan abubuwa cewa rikicin da ke faruwa a yankin Arewa gwamnati ba ta ga damar magance wannan matsalar ba. Tabbas haka ne gwamnatin Najeriya da ta ga damar magance matsalar kasa kamar Najeriya tunda manyan bariki da kwararrun sojoji na sama da kasa da na ruwa. Yanzu idan muka yi duba da irin abin da sojojin kamaru suka yi wa ‘yan ta’addar boko haram, suka fatattakesu da jiragen sama, har yanzu ba mu ji cewar Najeriya ta debo kwararrun sojojin ta ba,ta yarda za a ba su damar su je su shawo kan wannan lamarin duk da cewar ance Najeriya ta gyayyato masu leken asiri daga Amurka ko daga Ingila ne, wadanda aka ce za su gano duk motsin da wadannan ‘yan ta’adda suka yi. Duk wani dan Najeriya ya fahimci cewa gwamnati ba ta son kawo karshen wannan matsalar ta tsaro, a yankunan da rikici ya yi kamari, musamman Arewa maso gabashin Najeriya.
Idan muka yi la’akari da kundin tsarin kasashe da dama idan ana rikici to ko da anyi zabe a yankunan da ake tashin hankali idan ba zaman lafiya, to ana soke shi, sai a kirkiri dokar tabaci. Idan muka yi duba da abin da ake kira da dokar tabaci komai Yana tsayawa ne cak cikin jihar, inda za ka ga ko yankin mutum zai zama ba shi da ‘yancin zuwa wani wuri, ko aiki ko kasuwa, har ma da gona. Saboda idan ka ce wuri da dokar tabaci komai yana tsaye hatta mutum yana yawo idan an ba da damar kama shi.
Rashin yin zabe a wasu jahohin kasar magoya bayansa shugaban kasa su fito su fadawa ‘Yan Najeriya gaskiya. me yasa kasa kamar Najeriya ace wadannan mutane ‘yan ta’adda sun buwayesu Idan muka duba can cikin kudancin Kasar akwai bataliy-bataliya Wanda yau in Najeriya ta tashi kasashe suna iya mamayeta cikin kankanan lokaci yau ace, ‘yan mutane kadan sun buwaye ta ya kamata shugabani su fito su fadawa mutane gaskiya.
Batun zabe a Najeriya ban yi tsammanin cewa zai yiwu ba. Shin irin wannan hali masu madafun iko suke nema suka ki kai rundunonin soja, wanda ya zamanto sojin da aka kai na hadin gwiwa, wadanda suka hada da kasar Kamaru da Chadi da Nijar da ita kanta Najeriya, an ce wadannan ‘yan ta’addar sun kore su. Wannan shi yake nuna ba za a yi zabe a jihohi ukun da suka hada da Barno da Yobe da Adamawa.
Iidan ba a manta ba, irin wannan ta faru a kasar Mali, suka ki korar ‘yan ta’addar kasar suka yi zabe a haka. Duk yayin da aka ce an yi zabe a kasa a ce har jiha uku aki yin zabe, to za su ga an mai da su saniyar ware. Duk shugaban kasar da ya zo za su ga kamar babu ruwansu da shi, ganin ba a shiga zabe da su ba.
A gaskiya irin wannan rikicin ba bakon Abu bane ga nahiyar Afrika ba idan Akace da soja da dan ta’adda ai zuciyarsu ba daya bace. saboda shi Dan Ta’adda tun a duniya an nunamasa cewa duk abin da ya yi a doron duniya Aljannah zashi kuma idan akayi duba da irin kudin da suke samu Wanda zasuci da iyalansu za’a ce musu koda sun mutu za’a dauki nauyin iyalansu Idan muka duba irin haka Ta faru a kasar “Somaliya har yanzu tananan bata koma kasa ba. hakama kasar Aljeriya tun shekara ta 1990 suke fama da irin wannan matsalar duba da rin karfin da sojojin su suke dasu a Duniya, haka Idan kaje kasashen larabawa Afghanistan,Iraki.
Babban abin takaici kowa na jin irin furucin da Dakubo Asari yake yi akan zaben 2015 Yana cewa idan Jonathan bai ci zabe ba za a yi rikici, amma mahukunta sun zuba masa ido. Haka a ranar 15/12/2014 gidan rediyon Faransa ta yi wani Labarin cewa tsohon dan bindiga na yankin Neja-Delta a Najeriya, Cif Gobernment Ekpemupolo da aka fi sani da Tompolo, ya shiga da wasu wasu jiragen ruwan yaki bakwai zuwa kasar. Wannan ya jefa fargaba a zukatan ‘yan kasar,
musamman ma mazauna yankin na Neja-Delta mai arzikin man fetur, da aka dade ana fama da rikice-rikice. A labaran an sanar cewa an sayo jiragen ruwan ne daga kasar Norway, ta hannun wani kamfani mai zaman kansa a madadin kamfanin Global West bessel Serbices, mallakin Tompolo. idan ba ku manta ba Tompolo na daya daga cikin tsagerun yankin Neja Delta da suka amince su ajiye makamansu, sakamakon afuwar da hukumomin Najeriya suka yi musu a shekarar 2009.
A halin yanzu dai kamfanin Tompolo na da kwangilar miliyoyion Nairori da gwamnatin tarayya ta ba shi, don kula da mashigan ruwan, da nufin hana satar mai. Masani kan Harkokin Tsaro Husaini Munguna ya sanar wa gidan rediyon Faransa, cewa ba wani mutum ko kamfanin da ke da damar sayo jiragen yaki ba tare da hannun gwamnati ba, sai dai hukumomin tsaron kasar su sayo da kansu. Husaini Munguno a lokacin ya nemi a gudanar da bincike kan zargin. Har yanzu hukumomin tsaron, da na NIMASA da ke kula da tsaro a mashigan ruwan Najeriya, ba su ce komai ba, uwa uba gwamnati ta yi shiru kan lamarin.
Hukumar ‘Yan sanda ta kasa ta ce tana da jami’ai dubu 236000. In dai abin da suka fada gaskiya ne to mun yarda gaskiya ne. Daga cikin wannan kiyasin kusan dubu 21. suna gadin shugaban kasa da mataimakinsa dubu 19, suna gadin gwamnonin jihohi dubu 34 suna gadin bankuna masu rassa dubu da 6617 a kasa, sai dubu 18 masu tsayawa a hanya suna karbar taro da sisi a hannun mutane.
To idan muka duba za mu ga kusan ‘yan sanda dubu 1017 suna can suna aikin da ba su damu da tsaro ba, to yaushe ‘yan sanda dubu 10026 za su iya samar da tsaro ga jama’a kusan miliyan Dari da arba’in da uku wannan babban abun tambaya ne. Du wadannan Abubuwa Magana ce ta lokaci gamu ga Allah! Duk wanda baya jin tsoron Allah, baya jin kunyar mutane bai kamata a ji tsoronsa ba, balle ma a ji kunyarsa.Duk abin da yake tinkaho da shi Allah ya fi shi, kowane ne shi, ko dan wane ne. Allah ne kadai abin tsoro.

Anas Saminu Ja’en Makera, Muryar Talaka, Jihar Kano. 08188742103. 07033882307.