Babu shakka masu iya magana suna cewa ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Duk wanda ba shi da ilimi ya zama jahili, duk wanda ya zama jahili to ba shi da maraba da dabba. Saboda muhimmancin ilimi ya sanya mata ba a bar su a baya ba musamman ma matan aure wadanda suka san abin da suke yi sun dukufa wajen neman ilimin boko da na addinin muslunci.
Wannan yunkuri babu shakka zai taimaka kwarai da gaske wajen gina al’umma mai inganci, mai hangen nesa mai sanin yakamata da kuma kafa zuriya ta gari wacce za ta dunkule ta samar da al’umma mai cin gashin kanta tare da yin gogayya da sauran al’ummu da suka yi fice a ilimin addinin da na boko.
Hakazalika, matan aure na taka rawa sosai wajen bunkasar ilimin boko da na addini musamman ma a Arewacin Najeriya, saboda haka ya zama dole a jinjina musu to amma suna fuskantar matsaloli masu yawa wadanda idan ba a yi maganinsu ba to babu shakka za a yi asara mai yawa.
Babban kalubalen da matan aure ke fuskanta a hadahadar da suke yi ta neman ilimin boko sun hada da cin amana da wasu mazajensu suke yi musu na ganin sun samu ilimi kuma sun cimma burinsu na rayuwa. Sau da yawa za ka ga maza da dama za su yi wa mahaifan yarinya alkawari cewar idan sun aure su za su ba su damar ci gaba da karatunsu na boko amma da sun aure su sai su yi kememe su hana su. Wannan babbar matsala ce da ke ci wa matan tuwo a kwarya.
Wata matsalar ita ce ta yadda wasu mazan ke yi musu kafar Ungulu ta hanyar kin taimaka musu yayin da suke yin karatu tare da yi musu sassaucin aikin gida da kula da yara da kuma dafa abinci. Wasu mazan da zarar sun ga matarsu ta dage da karatu kuma sun ga lallai za ta kai wani mataki sai su fara jawo rikici a gida suna fakewa da dorawa matar laifin cewa ba ta kula da gida, ba ta dafa masa abinci kuma ba ta kula da ’ya’yansa. Daga nan sai ka ga hankalin matar ya tashi ta kasa samun kwanciyar hankali da nutsuwa. Daga nan sai karatun nata ya rika yin tangal-tangal. Har daga bisani ma wata sai ta daina karatun saboda tsoron kada aurenta ya salwanta.
Wata matsala da ke damun matan auren ita ce kyama da wasu ke nuna musu ta hanyar yi musu kallon tamkar matan da suka fi karfin mazajensu. Ita ma wannan matsala ce da ke ci wa matan auren tuwo a kwarya. Abin da ya kamata al’umma su gane shi ne don mutum ya bar matarsa tana neman ilimi bai zama cewa matarsa ta fi karfinsa ba. Hasali ma matan da suke da ilimi sun fi wadanda ba su da ilimi sanin kimar miji tare da sanin yadda za su kare hakkinsa ta kowace fuska.
Wata matsalar kuma it ace yadda wasu malaman makarantu ke musgunawa matan aure ko dai su kayar da su a jarabawa da gangan ko kuma su rika wahalar da su yayin da suke bincike na kammala karatun digiri na farko ko na biyu ko na uku. Sais u rika bata musu lokaci ta yadda za su hana su kammala binciken da suke yi a kan lokaci.
Shi iliimin boko da na addini idan suka hadu ga ’yan mace musamman matar aure za ka ganta da cikakken hankali da nutsuwa da sanin ya kamata da kuma iya lura da gida da tsafta da fasaha da hazaka tare da kuma da hangen nesa.
Saboda haka ya zama dole al’umma baki daya su tashi tsaye wajen tallafawa matan aure su sami ilimin boko da na addini don samun al’umma ta gari da ci gaban kasa da kuma bunkasar tattalin arziki. Kuma ya kamata gwamnati ta shigo cikin al’amarin don tallafawa matan aure su cimma burin da suka sanya a gaba na samun ingantaccen ilimi.