Salam Edita, don Allah ka ba ni dama nayi tsokaci dangane da irin matsalolin da sabon shugaban Najeriya wato Muhammadu Buhari zai tunkara bayan rantsar da shi. Tun daga cin hanci zuwa rashin aiki ga kuma uwa uba kwashe dukiyar talakawa ta inda zaka samu mutum daya ya kwashe dukiyar talakawa.
Tabbas hakan ya jawo mana talauci da karfin tsiya. Don haka mu talakawa muke ganin wannan lokacin shi ne zamu sami saukin radadin da muke fuskanta. Daga karshe muke kara yi wa Shugaba Buhari addu’ar Allah Ya raba shi da magauta wadanda suna nan sun zura idanu suga kuskurensa. Allah Ya tabbatar mana da adalci a wannan sabuwar gwamnatin da aka rantsar a yau Juma’a.
Daga Aminu Abdu Baka Noma, Kano, 08099479880.
Jinjina ga sabon Shugaba Muhammadu Buhari
Salam Edita, ka ba ni dama domin na yi jinjina ga Sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, bisa rantsar da shi kan karagar mulki a wannan muhimmiyar rana.
Shakka babu wannan ranar, babban tarihi ce ga al’ummar Najeriya, wanda jam’iyyar da suka zaba ta karbi mulki daga hannun jam’iyyar da ta shafe shekaru da dama, ba tare da shawo kan matsalolin da suka addabi ’yan kasar nan ba.
Daga karshe kirana ga sabon shugaban shi ne yakamata ya kwato dukiyar kasa daga hannun wadanda suka yi layar zana da ita domin kawai mallakawa kansu.
Daga Aminu dan-Kaduna Amanawa, 09035522212
Taya Shugaba Buhari murna
Assalamu alaikum Aminiya, don Allah ku ba ni dama na taya zababben Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari dangane da rantsuwar da ya yi ta kama aiki a yau Juma’a, Allah muke rokon Ya bai wa Buhari nisan kwana da ikon magance matsalolin da Jam’iyyar adawa a yanzu wato PDP ta tsunduma mu a ciki, Allah Ya bamu hakuri jure tsawon lokaci da za a dauka ana gyara don daidaita mana lamura.
Daga karshe nake bayyana goyon baya na ga ziyarar da Muhammadu Buhari yakai kasar Ingila, tare da fatan Allah Ya sa ta kasance mai amfani ga talakawan Najeriya.
Daga Sakatare Usman Bin-Affan Damaturu, 08038001563.
Mun gane makiyan talakawa
Zuwa ga Edita hakika yanzu mun gane masoyan Najeriya, mun gane makiya talakawan Najeriya domin cuta da keta aka hada na yajin aikin ma’aikatan man fetur ba kowa aka hadawa wannan ba sai sabon Shugaba Muhammadu Buhari. Tun da an kawar da PDP daga mulki shi ne ake son lalata komi kafin ya hau mulki domin kawai a kawo masa cikas tsakaninsa da talakkawan Najeriya. To ta Allah ba ta kuba don haka duk sherin da za ku yi wa Buhari Allah Ya na kare shi daga sherinku don haka kujera ku ga abin da zai biyo baya duk cutar da ’yan PDP suka aikata. Hakazalika, muna rokon gwamnonin APC da su binciki almundahanar da suka aikata ga ’yan Najeriya domin wallahi an cucemu.
Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi, 07061594299
Jinjina ga Aminiya
Assalamu alaikum jaridar Aminiya. Ina fata dukkan ma’aikatanku na cikin koshin lafiya. Na rubuto ne domin in jinjina muku game da namijin kokari da kuke yi na kawo mana labarai da rohotanai da dumi-duminsu, masu kayatarwa da ilmantarwa har ma da nishadantarwa. Ga shi kuna ba mu damar bayana ra’ayoyinmu a wannan jaridar mai farin jini. Allah Ya kara muku hazaka da basira, Ya kuma shige muku gaba.
Daga Mathew Garba, P.O BOd 8858, Kaduna, 081-72787278
Sako ga al’ummar Najeriya
Salam zuwa ga Editan wannan gida mai tarin albarka na jarida mai farin jini da tarin albarka ta Aminiya, ina muku fatan alheri, ina so don Allah a mika mini sakona da alummar Najeriya damu ma sabuwar gwamnati ta Muhammadu Buhari uzuri bayan an rantsar da shi ganin halin da kasar nan take ciki na tabarbarewar al’amura.
Daga Muhammad Ahmad idris, Kabuga Kano.
Ya dace sauran shugabanni su yi koyi da Buhari
Gwamnoni da sauran shugabanni a Najeriya yakamata ku yi koyi da Shugaba Muhammadu Buhari. Wajen yin tafiya zuwa kasashen wajen, inda Buharin yake yin tafiyar sa ba tare da ya kwashi dimbin mutane ’yan rakiya ba. Sabanin yadda wasu gwamnoni da shugabanni suke kwasar dimbin ’yan rakiya. Wanda yin hakan wata hanya ce ta barnar dukiyar kasa. Da fatan za ku yi koyi da Muhammadu Buhari.
Daga Haruna Muhammad Katsina, 07039205659