Salam zuwa ga Aminiya, Edita ina so ka ba ni dama na tambayi sarakunan kasar nan wai don Allah me ya sa ba sa ba wani mutum sarauta komai adalcinsa muddin ba ya rike da wani mukami na gwamnati walau a jiha ko a karamar hukuma ko kuma a tarayya. Babban misali shi ne kowa ya shaidi Janar Muhammadu Buhari mutum ne mai adalci da rikon amana, amma ban taba jin wani sarki ya yi yunkurin ba shi sarautar gargajiya ba. Amma da zarar an nada wani mutum a matsayin babban mukami a jiha ko tarayya to za ka ga sarakunan jikinsu na rawa wajen ba shi sauratar gargajiya ko da kuwa wannan mutum bai cancanta a ba shi wannan sarauta ta al’umma ba.
Allah Ka tsare mu
Allah muna rokonKa da ka yi mana sassauci a kan wadannan tashe-tashen hankulan da ke kokarin lahanta al’ummar Arewa, musanman na Arewa maso Gabas.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496
Kira ga al’umma
Salam Edita ka ba ni dama in shawarci jama’a da su guji shan gurbataccen ruwa kamar ruwan rafi musamman mutanenmu na karkara don guje wa kamuwa da cutar kwalara. Idan za a ci ganye a rika wanke shi da ruwan gishiri idan kuma za a dafa a rika dafa shi ya dafu. Idan an shiga ban daki a rike wanke hannu da sabulu ko omo. A rika tsaftace muhalli saboda rigakafi ya fi magani. Na gode.
kasimu Abdullahi Funtuwa Enb H. Officer 08063169007
Barka da Sallah
Assalamu Alaikum Edita, ka ba ni fili in taya Musulmin Najeriya Najeriya da na duniya barka da sallah. Allah Ya karbi ibadarmu tare da fatan mun yi sallah lafiya. Allah Ya zaunar da kasarmu Najeriya lafiya tare da karuwar arziki, amin. Nagode.
Alhaji kaseem 08176135707
Mu boye katin zabenmu da kyau
Edita, ka ba ni dama in yi kira ga ’yan Najeriya kowa ya boye katinsa na zabe kamar yadda zai boye kudi don yin zabe na gaba watau 2019. Yin haka ne zai kara ba mu damar zaben shugabanni nagari kamar yadda muka yi a yanzu.
Daga Baban Usman Katsina
Jinjina Ga EFCC
Edita, ka ba ni fili a cikin wannan jarida don in jinjinawa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) kan aikin da ta fara musamman na kama tsofaffin gwamnoni da wasu shugabannin gwamnati akan almundahanr da suka yi. Yanzu muka san za ki yi aiki tukuru babu fargabar komai.
Daga kaseem Malumfashi 08063169007
Duk abin da ka shuka, shi za ka girba
Aminiya, duk abin da mutum ya shuka to hakika shi zai girba. Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido karya ta kare, an saci kudin talakawa, giyar mulki ta debe ka kana zarewa talakawa ido, kana fadin maganganu yadda ka ga dama, yau an wayi gari ba kai kake mulki ba kuma an fara nuna maka rashin mutunci na kama ka kai da ’ya’yanka. Ina ganin ba ka ga komai ba, wani hukuncin sai a lahira.
Daga Kabiru Myball Sakkwato 08139498956
Ta’aziyyar Ga al’ummar Kukawa
Salam, Edita ka b a ni damar in isar da sakon ta’aziyya ga al’ummar Kukawa ta Jihar Barno da sauran sassan kasar nan da ke fama da hare-haren ’yan ta’adda, wanda hakan ke haifar da asarar rayuwa da dukiyoyin al’umma. Muna rokon Allah Ya jikan wadanda suka rasu, wadanda suka samu rauni kuma Allah Ya ba su sauki cikin gaggawa.
Daga dahiru Dauda (KGY) Bindawa
Jinjina Ga Amina Abdullahi
Aminiya ina mika sakon jinjina ga Amina Abdullahi wacce ta bayar da labarin Bishiyar mangwaro a shafin Manyan Gobe na jaridar Aminiya. Allah Ya kara basira amin.
Daga Muhammadu Sani wanda aka fi sani da Sani Bizy Boy Tafa
Ana musguna wa Hausawa a Legas!
Edita, don Allah Ka ba ni dama in mika kukanmu watau Hausawa mazauna Legas ga Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a kan yadda ake takura wa masu yin acaba Hausawa a Jihar Legas. Ana nuna bambanci wajen yin kame, idan Bayarbe ne ba a kama shi, amma da zarar an ga Bahaushe na yin acaba sai a garkame shi.
Daga Usaini Abdullahi karamar Hukumar Madobi Jihar Kano mazaunin Legas a karamar Hukumar Koshafe Ikoshi Isheri.
Akwai masu laifi a EFCC
Salam, Edita don Allah Ka ba ni dama in yi tsokaci a game da yadda Hukumar EFCC take kama tsofaffin gwamnoni. Ba tsofaffin gwamnoni ne kadai ke da laifi ba, su ma ma’aikatan EFCC din akwai marasa gaskiya a ciki.
Daga Abubakar Eti Kalgwai, Jigawa Auyo
Ta leko, ta koma!
Salam, Edita ina so ka ba ni dama in yi tsokaci game da dawowar sojojin yin bincike a kan hanyar Nyanya-Maraba. A kwanakin baya mun samu sa’ida amma yanzu abin ya sake kazancewa, ma’ana ta leko, ta koma ke nan. Yakamata sojoji su rika sassauta mana.
Daga Muhammad MD Direban Janway Kugbo, Abuja.
Aminiya ta yi kuskure
Salam, zuwa ga jaridar Aminiya mai farin jini. Bayan sallama ina so na sanar da ku wani kuskurre da kuka yi a jaridarku ta ranar Juma’a 10 ga watan Yuli 2015 a shafi na 6 a labarin Magidanci da ya karya hannun matarsa. Kuskuren shi ne inda kuka ce abin ya faru ne a karamar Hukumar Dutse ta Jihar Kaduna maimakon ta Jihar Jigawa. Da fatan za ku gyara.
Daga Shamsuddeen Ibrahim Fagwalawa (Ahalan) 07068126038
Ina son zama wakilinku a Jigawa
Salam, don Allah Edita ina so na zama wakilinku a Jigawa ta Gabas watau wajejen Kirikasanmu da Birniwa da Guri. Akwai labarai masu dadi amma babu wakili.
Daga Sani Idris Tela Dilmari.
Roko ga Janar Buhari
Salam, zuwa ga mai girma shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Muna rokon ka dauko mana Salomon Dalung ya zama shugaban Hukumar EFCC.
Daga Auwalu Shu’aibu Dandalama