A cikin makonnin nan muna ta nazari ne akan kalmar godiya ga Allah, wato nuna godiya ga Ubangiji a kowane irin hali da muka tsinci kan mu a ciki. A wannan makon da yardar Ubangiji za mu yi nazari ne akan nuna godiya ta wurin yabo da daukaka ko girmama Allah, domin bayan godiya, girman Allah ya isa yabo da daukaka, yin haka kuma zai kara mana sanin ikon Sa bisa rayuwar mu za mu kuma mori albarkun da ke kunshe cikin yin haka.
Nuna godiya da yabon Ubangiji wajibi ne ga dukan ’yan adam, domin shi ne mahalitcin mu, ta dalilinSa muke raye a yau. Ba mu da wani dalili da zai hana mu yin godiya ko yabonSa. Ubangiji Allah Ya cancanci yabo Shi ne dalili. Ku yabi Ubangiji dukkanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! (Zabura 150:6).
Ubangiji Allah Shi ne farko da kuma karshe, Sarkin sarakuna ne Shi, Allahn alloli, mahaliccinmu, mai biyan bukatun mu, mai ceton mu, mai kariyar mu, mai girma, babu kalma da za ta iya kwatanta girman Allah.
Bari mu ga abin da littafi mai tsarki ke fadi a nan; Ku raira waka ga Ubangiji, ku dukkan duniya, Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana. Ku yi shelar daukakarsa ga al’ummai, da ayyukansa masu girma ga dukan mutane, Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi, dole mu ji tsoronSa fiye da dukkan alloli. Gama allolin dukkan sauran al’umma gumaka ne, amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai. Daraja da daukaka suna kewaye da shi, iko da farin ciki sun cika hankalinsa. Ku yi yabon Ubangiji, ku dukkan mutanen duniya, Ku yabi daukakarsa da ikonSa! (1 Tarihi 16:23-28).
Bari mu duba wadanne albarku ne ke kunshe cikin yabo da daukaka Ubangiji Allah?
Misali, kamar yadda muka sani, a fadar sarakunan mu ko a bukukuwa sau da dama za mu ga wasu makada na yabo, suna kida suna kirari don a yi masu kyautar kudi, hakan nan a wasu wuraren ayukanmu akan bada lambar yabo idan ka yi aikin da ya cancanci yabo ko kuwa wasu makarantu ma na bada wannan idan ka ci nasara a jarabawar ka ko gasa. A kwanankin baya shugaban kasa ya bai wa wasu lambar yabo don kokari da aikin da suka yi wa kasar mu. A ganin ka, yaya za ka ji idan kana daya daga cikin masu karbar wannan lambar yabo? Babu shakka za ka yi matukar farin ciki.
Haka nan yake ga kowa, haka kuma duk lokacin da muka budi baki don yabon Ubangiji da zuciya daya muka kuma daukaka girmanSa da ikon sa, Ubangiji Allah na yin matukar farin ciki da mu. Ya kan sanya mana albarkunsa mara adadi, ya kawo mu kurkusa da Shi, ya kuma kare mu daga miyagun ayyukan shaidan kamar yadda za mu gani a cikin littafi mai tsarki don karin bayyani;
Ayyukan Manzanni 16: 25, 26 na cewa; A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna wakokin yabon Allah, ’yan sarka kuwa suna sauraronsu, farat daya, sai aka yi wata babbar rawar kasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan kofofin suka bubbube, marin kowa kuma ya kwance.
Kamar yadda Bulus da Sila suka shiga irin wannan matsanancin hali na shiga kurkuku, kana iya shiga wani matsanancin hali na damuwa, tsoro, rashin lafiya, da dai makamantan su wanda karfin ka ko basirar ka kan iya kasa fitar da kai. A wannan lokacin kada ka bar matsalar da kake ciki ta danne ka, sai ka tuna da maganar Ubangiji Allah masanin komai, ka yabe Shi domin girmanSa da ikonSa a cikin kowane hali, Shi da ya fi ka sanin matsalar da kake ciki, Shi kuwa zai fitar da kai daga wannan hali. A cikin littafi mai tsarki (2 Samaila 22: 47-50) Sarki Dauda ya nuna ikon godiya da yabon Ubangiji;
“Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa! Allah ne kakkarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa! Ya ba ni nasara a kan abokan gabana, Ya sa mutane a karkashin mulkina, Ya kubutar da ni daga hannun makiya. Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan makiyana, Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali. Domin wannan zan yi yabonka cikin al’ummai, Zan raira yabbai gare ka”. A nan ma mun ga yadda kariya da albarka kan zo bisa duk mai nuna godiya da yabo ga Ubangiji Allah.
Shi ya sa littafi mai tsarki na cewa:
Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa! Ku yabi karfinSa a sama! Ku yabe shi saboda manyan abubuwa wadanda Ya aikata! Ku yabi mafificin girmanSa! Ku yabe Shi da kakaki! Ku yabe Shi da garayu da molaye! Ku yabe Shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe Shi da garayu da sarewa! Ku yabe Shi da kuge! Ku yabe Shi da kuge masu amo! Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! ( Zabura 150:1-6).
Haka nan yabon Ubangiji yakan zama bishara ne ga wadanda ba su san Shi ba kamar yadda Bulus da Sila suka yi a kurkuku, dukan wadanda suke cikin kurkukun a wancan lokacin sun ga iko da girman Allah a lokacin da su Bulus suka fara raira wakar yabo [ga Allah]; an yi girgizar kasa mai karfi, kofofin kurkukun sun bude, hatta mai kulla da kurkukun ya samu ceto.
Bari rayuwan mu ta zama abu ne da zai kawo mutane zuwa ga sanin Ubangiji. Bari mu zama masu godiya da yabo ga Ubangiji a kodayaushe. Ta wurin yin haka kuma albarkunSa ba za su taba fasa zuwa garemu ba.
Abin tambaya a nan shi ne, a wani lokaci ne kake nuna godiya da yabo ga Ubangiji, ko sai lokacin da ka samu wani alheri? Idan fa haka ne, sai ka yi nazari akan abin da littafi mai tsarki ya koya mana a nan, godiya da yabon Allah ba shi da lokaci – abu ne da za mu yi a kowane lokaci domin yabon Ubangiji na tattare da albarka mai yawa da kan karfafa rayuwar mutum a kodayaushe. Bari mu ci moriyar wannan zarafi tun muna raye. Ubangiji Allah Ya ba mu ikon yabonSa da dukkan tsawon rayuwarmu, Amin.
Kalmar Godiya (4)
A cikin makonnin nan muna ta nazari ne akan kalmar godiya ga Allah, wato nuna godiya ga Ubangiji a kowane irin hali da muka tsinci…