✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalaman minista Kachikwu kuskure ne – Umaru Dembo

Minista a Ma’aikatar Man Fetur ta kasa Dokta Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa za a ci gaba da samun dogayen layuka a gidajen har karshen…

Minista a Ma’aikatar Man Fetur ta kasa Dokta Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa za a ci gaba da samun dogayen layuka a gidajen har karshen watan Mayu kuma shi ba zai iya yin dabo ba wajen shawo kan matsalar karancin mai, kalaman da suka taimaka wajen kara dagula al’amuran matsalar mai a kasar nan. Aminiya ta tattauna da tsohon Minista a Ma’aikatar Man Fetur Alhaji Ummaru Dembo domin jin ra’ayinsa game da cukuda lamurra da minista Kachiku ya yi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Maganar da Ministan Man Fetur ya yi Dokta Ibe Kachikwu da farko, inda ya ce za a dauki tsawon lokaci kafin matsalar man fetur ta kau, wannan lafazi nasa ya dace ko kuwa kuskure ne?
Abin dariya wai yaro ya tsinci hakuri,saboda duk abin da mutum yake yi na mulki yakamata ya yi da lura da sanin yakamata da mene bai kamata ba. Ba za ka yi abin da zai lalata harkokin da ake ciki ba, duk abin da za ka yi kuma za ka fade shi ba wai karya ka yi ba ,don kai kowane lokaci idan kana babba kana kan hanyar gyarawa ne. Ba ka ki a lokacin komai ya canza ba, kuma idan bai canza a lokacin ba, anjima bai yi ba, zuwa gobe, kullum kana kan abu zai yiwu ne kuma zai gyaru, kuma kana tunanin yadda za a yi a gyara. Saboda haka kowa dai da irin dabararsa, watakila shi yana ganin tasa dabarar ke nan, amma ga yawancin ’yan Najeriya kuma masu mulki da wanda kuma ya taba zama a irin wannan mukami a Najeriya,ya san cewa duk maganar da za ka yi ba za ka sako magana kawai yadda ka ga dama ba. Komai sai ka auna ka ga idan ka yi haka mai zai haifar kuma mai zai faru sannan ka yi maganarka, saboda haka ko wane dan Adam dai yana iya yin kuskure.
Aminiya: Ko kana ganin wannan maganar ta bai wa ’yan cuwa-cuwa dama ke nan su mike kafarsu ci karansu ba babbaka?
Ai abin da ya faru ke nan. Saboda yana gama fadin wannan maganar ina Abuja ranar nan, shi ke nan layuka suka tashi a gidajen mai ,masu jarkoki a kan hanya suka bullo ko’ina, to Abuja ma ke nan, balle sauran garuruwan da suke Najeriya. Tun daga lokacin har yanzu kullum abu sai da da baci yake yi.
Aminiya: A matsayinka na wanda ka taba rike wannan sashe wace shawara za ka bayar don a samu mafita?
Mu idan mun yi magana ma watakila a ce ’yan da ne, ba mu san abin da ake ciki yanzu ba, amma wuri ne wanda yake da abubuwa da yawan gaske kuma wanda yake bukatar kamar yadda aka ce yanzu shugaban kasa mai gaskiya, to ya kamata ya zabi masu gaskiya su ma su tafiyar da abubuwa, to akwai wani lokaci za ka ga kamar komai yana tafiya daidai lafiya lau, amma sai ka ga ashe akwai lauje cikin nadi. Babu wata shawara da za mu iya bayarwa tun da ba ma ciki ,sai dai wadanda  suke ciki su dudduba dukkan lungu da sako da suke ciki.
An ce mai daki shi ya san inda ruwa yake zuba masa, saboda haka su dudduba dukkan ma’aikatunsu su ga inda yake bukatar gyara ta yadda za a yi a samu waraka.
Aminiya: Akwai wasu wurare da za ka dan taba domin a sa su a kan hanya?
A’a, ai su sun san wuraren, wato sha’anin sayar da mai ka san ya hadu da cibiyoyi daban-daban, akwai kungiyar masu sai da mai, akwai manya-manyan kamfanoni, akwai kuma ita NNPC kanta, akwai su Depots, dukkansu suna tafiyarwa, akwai kuma masu tankokin mai na mota da suke diba.
Ka ga abubuwa ne da yawan gaske, sai an bi an gano wannan me e ciwonsa a gyara, shi kuma wannan mai ya dame shi, shi ma a gyara, idan ka bibiya tun daga NNPC inda ake shigo da mai, da Jeti din da ake bayarwa a aje da masu zuwa su saya da kungiyar su kansu masu sayar da mai na ’yan kasa da masu tankunan motoci da suke daukowa da masu gidajen mai da suke saidawa ,idan ka duba ko wane lungu akwai abin da za a iya dubawa kuma a gyara.
Aminiya: Wace shawara za ka ba talakawa da wannan abu ya shafa kai tsaye?
Babban abu shi ne a yi hakuri, domin idan suka lura da yadda aka samu mulkin an sha wuya, to a lura, kuma ga shi macuta da mabarnata da barayi ana tatse cikin wasu suna amayar da abin da suka sata, wasu ma ba su san ko gobe za su shiga jarum ba.