✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaka ya yi ritaya daga taka leda

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Brazil da Kungiyar A C Milan, Ricardo Kaka, ya sanarwar da cewa ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.…

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Brazil da Kungiyar A C Milan, Ricardo Kaka, ya sanarwar da cewa ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.

Mai kimanin shekara 35 da haihuwa, Kaka ya fara buga wasan kwallon kafa ne kimanin shekara 23 da suka gabata da kungiyar kwallon kafa ta Sao Poulo da ke Brazil.

Kaka, ya buga wasanni a manya-manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya kamar su: AC Milan, a kasar Itali, da kuma Real Madrid, ta Spain.

Kaka ya lashe kofuna kamar su kofin duniya, kofin zakarun Turai, gasar rukunin Serie A, kofin duniya na kungiyoyi, kofin rukunin Laliga da Copa del Rey na kasar Spain. Sannan kuma ya taba zama gwarzon dan wasan duniya a shekarar 2007. Kuma ya taba zama dan wasa mafi tsada a duniya bayan ya sanya hannu a kwantiragi da kungiyar Realmadrid na kimanin kudi Fam miliyan 56 a shekarar 2009.

Daga karshe Kaka, ya bugawa kungiyar Orlando City ne na kasar Amurka, sannan kuma ya sake komawa kungiyar da ya fara wasa ta Sao Polo a matsayin aro kafin ya yi ritaya.