✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ka’idojin rubutun Hausa (4): Rukunan nahwun Hausa  

A kasha da uku mun ji tarihin yadda aka fara aza ka’idojin rubutun Hausa sannan muka gangaro muka tabo bakaken rubutun Hausa da wasullansu. Yau…

A kasha da uku mun ji tarihin yadda aka fara aza ka’idojin rubutun Hausa sannan muka gangaro muka tabo bakaken rubutun Hausa da wasullansu.

Yau za mu fara duba bangarorin Nahwun Hausa, ma’ana kalmomin da suke iya haduwa su tayar da magana ta zama cikakkiya kuma daidaitacciya da za ta bayar da ma’ana.

Amma kafin nan ina tunatar da mu cewa, duk da bakin ‘P’ ba ya cikin bakaken rubutun Hausa, amma ana amfani da shi wajen rubuta sunan gari ko mutum da makamantansu. Misali Potiskum da Mudi Sipikin da sauransu.

Bangarorin kalmomin Nahwun Hausa

Hausa kamar sauran harsunan duniya tana amfani da wasu kalmomi da in sun hadu suke iya tayar da cikakkiyar jumla ta bayar da ma’ana tare da isar da sako ga mai sauraro ko mai karatu.

Wadannan kalmomi sun hada da:

 1. Suna
 2. Wakilin Suna/Lamiri
 3. Aikatau/Aiki, Fi’ili
 4. Siffatau/Siffa
 5. Bayanau
 6. Doguwar Mallaka
 7. Gajeriyar Mallaka
 8. Kalmomin Korewa
 9. Dirka
 10. Jakada
 11. Mafayyaci ko mafayyaciya
 12. Sauran kalmomi

 

 1. Suna:

Shi ne sunan da ake kiran mutum ko dabba ko wuri ko wani abu mai rai ko marar rai, kuma yana da rassa kamar haka:

 1. Sunan yanka ko ayyanannen suna:

Misali Ali, Abubakar, Fatima, Nusaiba, Amina, Zainab, Hajara, Tanko Danladi, Bala, Larai.

Wadannan sunaye ne na yanka ko wadanda ake kiran ayyanannun mutane da su, wadanda kana kiran sunan in akwai mai irin sunan zai waigo ya ga ko da shi kake yi.

Bari mu dauki kowane daya daga ciki mu sanya shi a jumla cikakkiya.

Ali ya tashi daga barci.

Abubakar ya zo.

Fatima ta wanke kwano.

Nusaiba da Amina ku share zaure.

Zainab da Hajara sun yi wanke-wanke.

Tanko da Danladi ku tafi gona.

Bala ya tafi makaranta.

Larai ta yi rubutu.

 

 1. Suna Gama-gari:

Misali: mutum, dabba, kwaro, gida, fartanya, wuka, lauje, aska, kandami, korama, gari, jiha, kasa da sauransu.

Wadannan sunaye ne da ba na wani ayyanannen mutum ko kwaro ko gida ko wani muhalli ko wani abu ba.

Misali:

Wani mutum ya wuce kasuwa.

Ali ya sayo akuya.

Wani kwaro ya fada min a ido.

Mu je gida.

Abubakar ya kai kudar fartanya.

Bala ya sayo wuka.

Ka sayo min lauje da aska.

Mu je korama debo ruwa.

In ka shiga gari ka sayo min alawa.

 

 1. Suna Gagara-Kirga:

Sukari, gishiri, yashi, ruwa da makamantansu.

Wadannan sunaye ne da ba a yi musu jam’i ko a fadi adadinsu. Amma ana iya yin jam’i ko bayyana adadin makunshinsu.

Buhun sukari.

Kwanon gishiri.

Yashi mai yawa.

Randar ruwa.

 

 1. Suna Tattarau:

Shi ne sunan da yake hado abubuwa ko mutane da yawa a ba su suna guda. Misali: Garke, bataliya, runduna.

Garken shanu.

Bataliyar sojin kasa.

Rundunar sojin sama.

 

 1. Wakilin Suna/Lamiri:

Wasu kalmomi ne da suke tsayawa a madadin suna ko su yi nuni ko ishara, mallaka ko tambaya, kuma sun kasu kamar haka:

 

 1. Rakabau: Misali: Ni, kai, ke, shi, ita, mu, ku, su.

Ni na sayo rigar.

Kai ka ba ta alawa.

Ke kika daka daddawar.

Shi ya zo da akuyar.

Ita ta zo da garin.

Mu muka sayo itacen.

Da ku aka share dakin.

Su suka tuka tuwo

 

 1. Madubi/ Inuwa: Kaina, kanka, kanki, kansa, kanmu kanku, kansu.

Na ga kaina a madubi.

Kai da kanka za ka kai kayan.

Ke da kanki za ki share dakin.

Ka sa ya kai da kansa.

Mu da kanmu za mu kawo shi.

Da kanku za ku yi rubutun.

Su da kansu za su debo ruwan.

 

iii. Zagin Aikatau:

Su ne kalmomin da suka kunshi: ya, ta, sun, yana, tana, za ta, kuke, suke da sauransu.

Misali:

– ya zo

ta tafi

sun rubuta

yana zuwa

tana dabe

suna karatu

za ta tafi

kuke yi

suke fada

 

 1. Nunau/Ishara:

Su ne kalmomin da suke nuna abu ko abubuwa a kusa ko nesa.

Misali: wannan, wancan, waccan, wadannan, wadancan.

Misali:

Wadannan kaya

Wancan mutum

Waccan yarinya

Wadannan littattafai

Wadancan yara

 

 1. Sunan mallaka:

Su ne kalmomin da suke nuna an yi wa mutum wani abu kamar: mani/mini, maka, miki, mana, muku, musu da sauransu.

Misali:

An saya mani/mini keke.

An yi maka dinki.

Za a yi mana kayan Sallah.

Ana dafa muku shinkafa.

Za a dafa musu tuwo.

 

Za a iya duba wadannan abubuwa don karin bayani a:

 1. Rayayyen Nahwun Hausa (2001) na Farfesa Hambali Junju.
 2. Koyar da alamomin ajiye magana a Hausa (2010), Takardar da Dokta Aliyu Mu’azu da Dokta Hafizu Miko Yakasai, suka gabatar a taron tattaunawa kan amfani da Daidaitacciyar Hausa a Jaridar Aminiya, a Abuja, ranar 25/2.2010.