✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka’idojin Rubutun Hausa (2): Tarihin rubutu a Hausar boko

Kamar yadda muka fada a kashi na farko, rubutu cikin harshen Hausa ya faro ne cikin Ajami kafin Turawa su kawo bakaken Ingilishi da muke…

Kamar yadda muka fada a kashi na farko, rubutu cikin harshen Hausa ya faro ne cikin Ajami kafin Turawa su kawo bakaken Ingilishi da muke kira da bakaken boko wadanda suka samo asali daga rubutun Latin.

A yau na leka wata tsohuwar ajiyata ta wata takarda da malaminmu Yusuf Baba Gar ya taba gabatar mana lokacin muna dalibai a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi mai taken: “Ka’idojin Rubutun Hausa, Auna Fahimta, Insha’i da Rubutun Wasika.”

Kamar yadda takardar ta kunsa, kafin mu tsunduma ga sanin ka’idojin rubutun Hausa, za mu dan waiwaya baya mu ga yadda tarihin rubutun Hausar boko ya samo asali.

Hakan zai ba mu damar sanin inda aka fito da inda ake ciki a yanzu da kuma kila inda za a nufa a fannin kiyaye ka’idojin rubutun Hausa a nan gaba.

A makon jiya mun ce rubutun Hausa ya samo asali ne daga rubutun Ajami ta dalilin zuwan Larabawa, sai kuma na Hausar boko ya zo ta dalilin zuwan Turawa, dukkansu biyun sun shigo ne ta dalilin ziyarce-ziyarce da yada addini ko dalilin kasuwanci.

To sai dai ba za mu yi magana a kan Ajami ba, saboda muna magana ce a kan rubutun boko.

Asalin rubutun Hausar boko

Rubuta Hausa a cikin bakaken boko ya samo asali ne tun wajen Karni na 17/18 lokacin da Turawan Mishan da ’yan kasuwa suka rika shigowa Nahiyar Afirka.

Turawan sun yi kokarin sanin harshen Hausa da al’adunsa kamar yadda suka yi a kan sauran harsunan da suka tarar, inda suka rika aika rahotannin abin da suka samu zuwa kasashenmu don a rika bugawa a mujallu da littattfai.

Kuma bincike ya nuna cewa an fara rubuta Hausa a cikin kalmomin boko ne a kasar Denmark a Karni na 18.

Yadda aka fara rubutun Hausar Boko

Sarkin Denmark na lokacin ne ya tura wakilansa zuwa kasashen Larabawa don su yi binciken kimiyya a 1773 Miladiyya, kuma a cikin wadanda ya tura akwai wani Bature mai suna B.G. Niebuhr.

Bayan wannan bincike sai wani Balaraben kasar Tunisiya mai suna Abdurrahman da wani bawansa mutumin Borno da ya ji Hausa suka kai ziyayar jakadanci kasar Denmark.

Niebuhr ya zama tafinta mai fassara tattaunawa a tsakanin Sarkin Denmark da Balaraben nan.

Sai abota ta shiga tsakanin Niebuhr da Balaraben, daga nan Niebuhr ya yi sha’awar koyon Hausa daga wancan bawan Balaraben.

Sakamakon haka B.G. Niebuhr ya dukufa ga koyon Hausa, bawan nan yana gaya masa sunayen abubuwa yana rubutawa da bakaken boko gwargwadon yadda ya ji muryar kalmomin tare da fassararsu.

Amma saboda rashin kwarerwasa a harshen da kuma rashin dokokin rubutun Hausa sai ya zamo bai rubuta kalmomin yadda suka kamata ba.

Wannan ya sa in aka dubi kalmomin da ya rubuta a wancan lokaci za a ga akwai kura-kurai a tsakanin yadda ake furta kalmomin da yadda ya rubuta su a cikin wani littafinsa mai suna: “The Life of Niebuhr” wanda aka buga a kasar Denmark a 1791, wato shekara 229 da suka gabata.

Misali, ga yadda ya rubuta wasu kalmomin:

  • Kalma        –      Yana nufin    –     Ingilishi
  1. Motum       –      Mutum           –     Man
  2. Koroma     –      Korama           –    Stream
  3. Ghurassa    –     Gurasa             –    Wheaten food
  4. Berni          –     Birni               –     Town
  5. Daua          –     Dawa              –    Guinea corn
  6. Shinkaffer  –     Shinkafa          –    Rice
  7. Sirki           –     Sarki                –    Emir/Chief
  8. Crua          –     Ruwa               –    Water

Bayan Niebur, a cikin Turawa masu ziyarar gano Afirka na farkon Karni na 19 wadanda suka yi rubuce-rubuce da Hausar boko, babu kamar Henric Barth da J.F. Schon.

Henric Barth da Kungiyar gano Afirka

Henric Barth Bajamushe ne da ya jagoranci kungiyar gano Afirka.

Sannan a tsakanin 1850 zuwa 1855 ne lokacin da yake tafiye-tafiyensa a Afirka ya hadu da wadansu samari biyu Dorugu da Abbega.

Dorugu Bahaushe ne haifaffen Damagaram a Jamhuriyyar Nijar, wanda tun yana yaro aka sayar da shi ga wani Balarabe a 1851.

Abbega kuma dan kabilar Margi ne daga Borno/Adamawa.

Henric Barth ya fanshi Dorugu da Abbega daga Balaraben, ya debe su ya tafi da su Tumbuktu a kasar Mali.

Daga nan ya zarce da su zuwa Ingila a 1855 inda suka rika koya masa Hausa suna ba shi labarai.

Sakamakon haka ne Barth ya rubuta wani littafi na musamman kan harsunan Hausa da Filatanci da Barbarci mai suna: “Collection of Vocabularies of Central African Languages, Gotha 1862.

’Yan mishan masu yada Kiristanci

Mista J.F. Schon shi ne gwarzon rubuce-rubuce cikin Hausar boko a Turai kafin Karni na 20.

An haife shi a Jamus a 1803, kuma ya mika kansa ga wata kungiyar yada addinin Kirista mai suna Church Missionary Society (CMS) wadda ta aiko shi kasar Saliyo a 1832 inda ya shekara bakwai yana aikin yada addinin Kirista yana hadawa da koyon harsunan Afirka a wurin ’yantattun bayi.

Schon ya koma Ingila a 1847 ya yi zamansa yana rubuta littattafai kan harshen Hausa da wasu harsunan Afirka.

Yana cikin aikin shi kadansa sai ya ci sa’a ya hadu da samarin nan biyu Dorugu da Abbega wadanda suka bi Henric Barth zuwa Ingila.

Schon ya nemi Barth ya ara masa su don su taimaka masa ya rika nazari kan harshen Hausa.

Barth ya yarje masa suka je wurin Schon suka zauna na shekara takwas suna taimakon sa yana rubuta littattafan Labarai da bayanai da Nahwun Hausa da Kamusun Hausa da kuma fassare-fassaren wasu littattafan addinin Kirista daga Ingilishi zuwa Hausa.

Schon ya rubuta littattafai da dama a kan Hausa wadanda suka zama littattafan yin nazari da koyon Hausa ga Turawa masu son zuwa Afirka.

Kuma wadannan littattafai ne suka zama harsashin gina rubutun Hausa a Karni na 20.

Wasu daga cikin littattafan su ne:

  • Schon J. F. Address to the Chiefs and People of Africa (in Hausa), Cape Coast, 1841.
  • Schon J. F. Farawa Letafen Magana Hausa, Berlin, 1857.
  • Schon J. F. Letafen Musa Nafari B.F.B.S, London 1858.
  • Schon J. F. Letafen Musa Nabi’u B.F.B.S, London 1858.
  • Schon J. F. Grammer of the Hausa Language, C.M.S. London, 1862.
  • Schon J. F. Dictionary of the Hausa Language, C.M.S, London, 1876.
  • Schon J. F. Hausa Reading Book, C.M.S. London 1877.
  • Schon J. F. Labari Nagari. C.M.S. London, 1877.
  • Schon J. F. Letafe No Alwasi Sabo. C.M.S. London 1880.
  • Schon J. F. Magana Hausa, S.P.C.K. London 1885.

Daga Salihu Makera – [email protected]