Rarraba kalmomi da hade su shi yake bambance wanda ya yi karatu kuma ya san ka’idojin rubutu da wanda bai yi karatu ba, kuma ya zama malamin kansa.
Yau za mu sake gabatar da abin da masana suka ce kan rarraba kalmomi ko hade su a yayin rubutun kamar haka:
a). Kada a hade wakilin suna da mafa’uli da kowace kalma, misali:
- Ya ki shi, ba yaki shi ba.
- Sun ja shi ba sun jashi ba.
- An roke ta ba an roketa ba.
b). Ana rubuta kalmomin jam’u a hade wato ana daukarsu a matsayin kalma guda ba kalmomi daban-daban ba.
- Misali: Ko’ina ba ko ina ba
- Koyaushe ba ko yaushe ba
- Kowadanne ba ko wadanne ba
- Kowanne ba ko wanne ba
- Kowace ba ko wace ba
- Komai ba ko mai ba
- Kowa ba ko wa ba
c). Ana rubuta zagagen fi’ili masu zuwa a hade
- Lokaci na sabo
- Nakan karanta ba na kan karanta ba
- Yakan karanta ba ya kan karanta ba
- Takan karanta ba ta kan karanta ba
- Mukan karanta ba mu kan karanta ba
- Sukan karanta ba su kan karanta ba
- Lokacin mai ci dogare
- Nake ba na ke ba
- Kake ba ka ke ba
- Kike ba ki ke ba
- Yake ba ya ke ba
- Take ba ta ke ba
- Muke ba mu ke ba
- Suke ba su ke ba
- da sauransu.
iii. A raba zagagen fi’ili masu nuna lokaci mai zuwa
- Za mu tafi ba zamu tafi ba
- Za ka tafi ba zaka tafi ba
- Za ki tafi ba zaki tafi ba
- Za ku tafi ba zaku tafi ba
- Za mu tafi ba zamu tafi ba
- Za su tafi ba zasu tafi ba
Sai dai an amince a hade lamirin lokaci ‘za’ da lamirin mutum in an yi amfani da lamirin mai magana shi kadai, saboda an amince da ‘zan tafi’ da ‘zai tafi’ maimakon ‘za na tafi’ ko ‘za ya tafi.’
iv. Manunin lokaci shudadde
Na yi ba nayi ba
- Ka sha ba kasha ba
- Kin ce ba kince ba
- Mun je ba munje ba
- An ki ba anki ba
- Kun ci ba kunci ba
- Kin yi ba ba kinyi ba
- Sun sa ba sunsa ba
- Da sauransu
- v. Ana rubuta manunin lokacin ci gaba a hade
- Ina yi ba i na yi ba
- Kana ya ba ka na yi ba
- Tana yi ba ta na yi ba
- Yana yi ba ya na yi ba
- Muna yi ba mu na yi ba
- Suna yi ba su na yi ba
- Nake yi ba na ke yi ba
- Yake yi ba ya ke yi ba
- Take yi ba ta ke yi ba
- Muke yi ba mu ke yi ba
- Kuke yi ba ku ke yi ba
- Suke yi ba su ke yi ba
- Manunin lokaci mai zuwa ana raba su ne
- Zan zo ba zanzo ba
- Za ki yi ba zaki yi ba
- Za ta yi ba zata yi ba
- Za mu yi ba zamu yi ba
- Za ku yi ba zaku yi ba
- Za su yi ba zasu yi ba
- Za a yi ba za’a yi ba
vii. Ana raba kalmomin ma’aunin lokaci umartau
- In yi ba inyi ba
- Ka yi ba kayi ba
- Ki yi ba kiyi ba
- Ya yi ba yayi ba
- Ku yi ba kuyi ba
- Mu yi ba muyi ba
- Su yi ba suyi ba
d). Ana rubuta wadannan kalmomi a hade kamar haka:
- Saboda ba sabo da ba
- Watakila ba wata kila ba
- Abin da ba abinda ba
- Wane ne ba wanene ba
- Wace ce ba wacece ba
- Mene ne ba menene ba
- Mece ce ba mecece ba
- e) A raba wadannan kalmomi masu zuwa yayin rubutu
- Ni ne ba nine ba
- Ni ce ba nice ba
- Kai ne ba kaine ba
- Ke ce ba kece ba
- Shi ne ba shine ba
- Su ne ba sune ba
- Ita ce ba itace ba
- Mu ne ba mune ba
- Su ne ba sune ba
- Na yi ba nayi ba
- Mun yi ba munyi ba
- Ya ce ba yace ba
- Ya fi ba yafi ba
- Ta fi ba tafi ba
- Ya ki ba yaki ba
f). A hade kalmomi masu zuwa yayin rubutu
- Mini ba mi ni ba
- Maka ba ma ka ba
- Muku ba mu ku ba
- Musu ba mu su ba
- Nawa ba na wa ba
- Naki ba na ki ba
- Namu ba na mu ba
- Taku ba ta ku ba
- Nasu ba na su ba
- Tasu ba ta su ba