✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kai ya rabu tsakanin Hukumar Tace fina-finai da MOPPAN kan yafe wa Rahama Sadau

A kwabakin baya ne fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta nemi afuwar Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano…

A kwabakin baya ne fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta nemi afuwar Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II bisa fitowar da ta yi a wani faifan bidiyon waka tare da mawaki Classik wanda ya jawo mata kora gaba daya daga masana’antar fina-finan Hausa na Kannywood a bara.

“Sunana Rahama Sadau ina so in yi wasu bayanai a kan abubuwan da suka faru a baya wanda ya bata ran mutane masu yawa. A wancan lokaci na yi shiru ne don ba na son yin magana a lokacin da abin yake kan zafinsa. Wani dalilin kuma da ya ahan ni magana shi ne ba ni son idan manyan sun yi fushi na yi magana a wannan lokai ba, a ganina idan na yi haka kamar na saba musu ne”

“Ina bayar da hakuri ga duk wanda bai ji dadin abin da na aikata ba musamman Sarkin Kano da Gwamnan Kano da abokan aikina a masana’antar fim din Hausa da duk wanda bai ji dadin lamarin ba”

Rahama Sadau ta kara da cewa “idan aka sami faruwar wani abu mara kyau ba wai kawai ga Rahma Sadau ba, ga duk wani dan fim, abin da muke bukata shi ne goyon baya da kuma karfin gwiwa ta yadda za a kira mu a nuna mana kuskurenmu domn mu gyra amma ba wai a je na gulmarmu akan abin ba. Ina amfani da wannan dama waje rokon kowa ya yafe min kan abin da ya faru, insha Allah ba zai kara faruwa ba”

Idan za a iya tunawa kungiyar MOPPAN ta yanke hukuncin korar jaruma Rahma Sadau daga masana’antar fim din Hausa a ranar 2 ga watan Oktobar shekarar 2016 ne bisa zargin ta da laifin mummunar fitowa a faifan bidiyon wakar Hausa tare da mawakinan mazaunin garin Jos wato Classik.

Sai dai wannan neman afuwa da jaruma Rahama ta yi tabar baya da kura domin hakan ya jawo sabani tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da kuma kungiyar Yan fim ta MOPPAN wacce ita ce ta kori Rahaman, Daga lokacin da Rahamar Sadau din ta yi wannan tuba Hukumar Ta ce fin-finai ta Jihart Kano karkashin jagoranci Isma’ila Na’abba Afakallah ta bayyana cewa ta karbi wannan tuba na Rahama domin a cewarta matar na tuba ba ta rasa mijin aure, kuma duba da cewa duk dan adam ajizi ne don haka ta yafe wa jarumar.

Afakallah ya bayyana cewa duba da cewa Rahaman ta yi da-na-sani game da abin da ta aikata hukumarsa ta yafe mata ta kuma dage takunkumi da aka kababa mata, don haka za ta ci gaba da duba mata finafinainta kamar yada take duba na sauran abokan sana’arta ‘yan fim. “Ta zo da kanta ta nemi afuwa cewa ta gane kuskurenta muka ba ta umarni da ta je ta nemi afuwar al’ummar malam Bahause da take wakilta hakuri. Sannan muka umarce ta da ta ba Mai marataba Sarkin Kano da Gwmanan Kano hakuri sannan muka umarce ta ta ba kungiyarta hakuri ta hanyar rubuta takarda, wanda kuma ta aikata dukkanin abubuwan d amuka umarce ta da su. A matsayinmu na Hukumar Tace finafinai bisa wanann sharadi da ta cika muke ganin ya kamata mu ci gaba da duba finafinanta kamar yadda muke duba fim din kowa”

Wannan kalamai na Shugaban Hukumar Tace Finafinai ba ta yi wa bangaren kungiyar MOPPAN dadi ba, don haka ta hau kujerar na-ki, inda ta ce ita fa har yanzu a wajenta jaruma rahama Sadau korarriya ce.

Shugaban kungiyar ta MOPPAN Kabiru Maikaba ya jaddada cewa kungiyarsu ba ta karbi tuban na Rahama ba. Kabiru Maikaba ya ce yafiyar da Afakallah ya y i wa Rahama ya yi ta ne don kashin kansa, amma ba da yawun kungiyar tasu ba. “kungiya ce ta dakatar da ita kuma kungiyar ce take da alhakin dawowa da ita. Mu a matsayinmu na kungiya ba mu dawo da ita ba. Abin da muka sani har yanzu Rahama Sadau korarriya ce”

A cewar Kabiru Maikaba “yafiyar da Afkallah ya yi mata ya y i ne kawai a karan kansa.kuma yana magana ne a kan hukumarsa. Kuma maganar da yake yi cewa za su ci gaba da duba mata finafinanta ba ta bisa ka’ida. Za mu zauna da shi mu tattauna a kan hakan, domin a gaskiya idan ya yi haka bai kyauta ba”