✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kai tsaye: Manchester United ta lallasa Manchester City da ci 3 da 2

A zagaye na farko Man City ta zura kwallaye biyu, inda Vincent Kompany da I. Gundogan suka zura kwallayen. Sai kuma a zagaye na biyu…

A zagaye na farko Man City ta zura kwallaye biyu, inda Vincent Kompany da I. Gundogan suka zura kwallayen. Sai kuma a zagaye na biyu Man United suka farke, inda Paul Pogba ya zura kwallaye biyu, sannan Chris Smalling ya zura na ukun.

A wasan, Man  City ta kai hari sau 6, ita kuma Man U ta kai hari sau 4. Amma dai Man United din ce ta sau nasarar zura kwallaye har uku.

Alkalin wasa ya busa. An kammala wasa. A takaice dai Man United ta bata wa Man City biki yau. Koda yake cewa za su daga kofin, amma bai Man United sun ce lallai fa ba a kansu ba kuma ba yau ba.

Saura minti biyu kacal a tashi wasa. Har yanzu dai Man United ce ke gaba. 3 da 2

An kara minti biyar. Har yanzu dai abin hakanan yake.

Saura minti kacal. Har yanzu dai Man U 3 Man City 2.

A yanzu haka ana ci gaba da hammata iska tsakanin kungiyar  Man United da Man City a gidan Man City. Idan dai har Man City ta lashe wannan wasa, to shi ke nan ta lashe kofin firimiya na bana.

yanzu haka ana minti na 77, kuma Man United ce ke da kwallaye 3 yayin da ita kuma Man City ke da kwallaye 2