Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce babu gaskiya a rahotanni da ke cewa an yi garkuwa da wasu mutane a babban titin Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Umar Musa Muri da kuma Kanar Ibrahim Gamnari, kwamandan rundunar Operation thunder strike suka jagoranci ”yan jarida zuwa kauyen da rahotannin suka ce abun ya faru inda suka tattauna da mazauna.
Aruwan ya ce babu wanda aka yi garkuwa da shi a ranar ta jajibirin Babbar Sallah.
“Binciken da muka yi ya gano cewa babu wani abun da ya faru ranar Alhamis a hanyar. Muna so mutane su sani cewa akwai matakan tsaro da yawa daga Hedikwatar Tsaro ta kasa.
“Ba mu ce babu matsalar tsaro ba, amma muna aiki ba dare ba rana domin magance su, kuma muna samun nasara.
Ya ce akwai isasshen tsaro a titin Kaduna zuwa Abuja ga matafiya da masu ababen hawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi kira ga masu yada jita-jita su daina
A ranar Alhamis wasu kafofin labarai na intanet sun kawo rahoton zargin yin garkuwa da wasu mutane a kan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna a daidai Katari inda aka ga wata mota a yashe.