✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kaduna da Kebbi da Zamfara ba su samu Manyan Sakatarorin Tarayya ba

Jihohin Kaduna da Kebbi da Zamfara da Kuma Ribas ba su samu gurabu ba a mukaman Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya 12 da Shugaba Buhari ya…

Jihohin Kaduna da Kebbi da Zamfara da Kuma Ribas ba su samu gurabu ba a mukaman Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya 12 da Shugaba Buhari ya nada.

Sanarwar da Ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ya fitar bai nuna sunanyen sabbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya daga jihohin hudu ba.

A baya dai ofishin ya nuna akwai gurabu 16 na sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da za a nada daga cikin daraktoci 41 da suka yi jarabawa a makonnin baya.

Amma jerin sunayen da aka fitar ranar Talata bai bayyana dalilin rashin sanya sunayen wakilan jihohin Zamfara, Kebbi, Kaduna da kuma Riabs ba.

Mutum 12 da aka nada da jihohhinsu su ne:

 • Akinlade Oluwatoyin- Kogi.
 • Alkali Bashir Nura- Kano.
 • Anyanwutaku Adaora lfeoma- Anambra.
 • Ardo Babayo Kumo- Gombe.
 • Belgore Shuaib Mohammad Lomido- Kwara.
 • Ekpa Anthonia Akpabio- Kuros Riba.
 • Hussaini Babangida- Jigawa.
 • Mahmuda Mamman- Yobe.
 • Meribole Emmanuel Chukwuemeka- Abia.
 • Mohammed Aliyu Ganda- Sokoto.
 • Tarfa Yerima Peter – Adamawa.
 • Udoh Moniloja Omokunmi-

Sanarwar daga babbar jami’ar sadarwar ofishin ta ce nan gaba za a sanar da ranar da za a rantsar da sabbin manyan sakaratorin.