Wata alkalin kotun tafi da gidanka a jihar Kaduna ta sha da kyar, ta kuma yi gudun ceton rai a lokacin da wani sashi na ‘yan sandan da ke aiki da kotun suka ba hammata iska da wasu gungun sojojin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a garin Zariya bayan da kotun tafi da gidan ka wacce aka kafa domin hukunta masu saba dokar kulle a jihar Kaduna, ta ci tarar wani soji da ke aiki da rundunar ta Depot Naira dubu goma.
Majiyar Aminiya ta shaida cewa sojin wanda a lokacin ba ya cikin kakinsa na soji ya tambayi dalilin da yasa aka ci tarar tasa, ko da wani dan sanda da ke kusa da wajen yaji yana tambaya sai ya kaure shi da mari.
Wani da ya shaida lamarin yace, “da wasu sojoji suka ga dan sandan ya mari abokin aikin su, sai suka shigar masa, inda aka kaure da fada lamarin da ya sanya alkalin kutu ta gudu don ceton ran ta”
Da yake magana akan lamarin mai taimakawa daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Kaftin Audu Arigu ya shaida cewa zuwa yanzu sun sasanta lamarin.
” Yanzu haka ma muna tare da dan sandan a nan barikin mu a Depot,” in ji shi.