✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada soyayyarmu ga Annabi ta tsaya a fatar baki (1)

Daga Muhammad Habibullah Muhammad Shakidiy Fassarar Salihu Makera, Mukaddima Bayan haka ya bayin Allah! Hakika Allah Ya yi mana rahama mayalwaciya sakamakon kebe mu da…

Daga Muhammad Habibullah Muhammad Shakidiy

Fassarar Salihu Makera, Mukaddima

Bayan haka ya bayin Allah! Hakika Allah Ya yi mana rahama mayalwaciya sakamakon kebe mu da sanya mu mabiya mafi alherin halitta (Annabi Muhammad SAW), wanda ya fitar da mu daga duffan kafirci da zalunci zuwa ga hasken imani, ya fitar da mu daga bata zuwa ga shiriya ya fitar da mu daga tabewa zuwa ga sa’ada daga kaskanci da zalunci da jahilci da rarrabuwa da wulakanci zuwa ga daukaka da adalci da haduwar kai da karimci. Shin yaya za mu kasance ba domin addinin Annabi Muhammad (SAW) da akidarsa ba? Wace kima za mu yi in ba domin sakonsa da shari’arsa ba? Wace makoma muke da ita in ba domin da’awarsa ba? “Lallai ne hakika, Allah Ya yi babbar falala a kan muminai, domin Ya aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littafi da Hikima, kuma lallai sun kasance daga gabani, hakika suna cikin bata bayyananniya.” (K:3:164).

Ya isar da sako mafi kyan isarwa, ya bayar da amana, kuma ya yi nasiha ga al’umma, kuma ya yi kokari a cikin yada addinin Allah iyakar kokarinsa. Mutanensa sun cutar da shi, amma ya yi hakuri domin ya isar da wannan sako. Ya tafi zuwa Da’ifa a kafa yana gabatar da Musulunci ga kabilunta, amma suka sanya kananan yaransu suka rika jifarsa suka raunata shi a kafarsa amma ya yi hakuri don isar da da’awarsa. Ya rika zuwa ga kabilun Larabawa suna korarsa, sai dai irin wannan bai kashe masa gwiwa ba. An rika azabtar da sahabbansa a cikin zafin rana suna masu igasa da neman taimakon Allah Madaukaki saboda wannan addini. Har ta kai an umarce shi da yin hijira daga birnin Makka inda ya tsaya a wajen Makka yana cewa: “Wallahi ke ce mafi soyuwar bigire zuwa ga Allah. Kuma wallahi ke ce mafi soyuwar bigire a wurina, ba domin mutanenki sun fitar da ni ba, da ban fita ba!”

Wata rana an fasa masa kai, an karya masa hakoran gaba, makiya sun yi yunkurin kashe shi a Yakin Khandak, inda suka tura rundunoni domin neman kansa. Yahudawa sun sanya masa guba a abinci, sun yi masa sammu, sun yi kokarin kashe shi a lokuta da dama. Sai dai wannan bai sanyaya azamarsa ta yada wannan addini ba, har sai da Musulunci ya isa mahudar rana da mafadarta.

Ba za a iya kirga falalolinsa ba, kuma martabobinsa ba za su kididdigu ba. Babu wata siffar kamala face ya siffatu da ita (SAW). Allah Ya tsarkake hankalinsa inda Ya ce: “Ma’abucinku bai bata ba, kuma bai ketare haddi ba.” (K:53:2). Kuma Ya tsarkake harshensa inda Ya ce: “Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa.” (K:53:3). Kuma Ya tsarkake shari’arsa inda Ya ce: “(Maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa.” (K:53:4). Kuma Ya tsarkake mai karantar da shi inda Ya ce: (Mala’ika) Mai tsananin karfi ya sanar da shi. Ma’abucin karfi da kwarjini, sa’an nan ya daidaita.” (K:53:5-6). Kuma Ya tsarkake zuciyarsa inda Ya ce: “Zuciyar (Annabi) ba ta karyata abin da ya gani ba.” (K:53:11). Kuma Ya tsakake ganinsa inda Ya ce: “Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ketare haddi ba.” (K:53:17). Kuma Ya tsarkake sahabbansa inda Ya ce: “Kuma wadannan da suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu.” (K:48:29). Kuma Ya tsarkake shi gaba dayansa inda Ya ce: “Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki manya.” (K:68:4).

Kuma Ya jingina shi da risala inda Ya ce: “Muhammadu Manzon Allah ne.” (K:48:29). Kuma Ya kira shi da sunan annabta inda Ya ce: “Ya kai Annabi!” (K:60:12). Kuma Ya daukaka shi da bauta inda Ya ce: “Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi tafiyar dare da bawanSa.” (K:17:1). Kuma Ya yi masa shaida da tsayuwa da ibada inda Ya ce: “Kuma lallai ne shi a lokacin da bawan Allah ya tsayu yana kiranSa.” (K:72:19).

Allah Ya budada masa kirjinsa Ya dauke masa nauyinsa, Ya daukaka ambatonsa Ya cika al’amarinsa Ya kammala addininsa da shi, Ya sanya damarsa mai da’a. Ubangijinsa bai yi masa ban-kwana ba, kuma bai ki shi ba. Sai dai Ya same shi ba ya da shari’a, sai Ya shiryar da shi. Ya same shi fakiri Ya wadatar da shi. Kuma Ya same shi maraya Ya yi masa makoma. Ya ba shi zabi tsakanin dauwama a duniya da haduwa da Shi, sai ya zabi haduwa da Majibincinsa ya ce: “Na zabi haduwa da Madaukaki.”

Na rantse da Allah wata mace ba ta yi ciki ko ta haifi,

Kamar Manzo, Annabin al’umma mai shiryarwa ba.

Sai ga shi wata rana ta zo, wadansu mutane da ba su san Allah ba koda daidai da sa’a daya suna rayuwa cikin duffan sha’awoyi, manufofinsu da tunaninsu da akidojinsu batattu suna kokarin karkata daga wannan haske.

Misali a shekarun baya, wata jaridar Denmark da sauransu sun buga zanen hoto na isgilanci ga mafificin halitta daukacin Musulmi na ji na gani, ina kishin addinin? Ina son Manzon (SAW)? Ina kare shi? Ashe ba wannan ne matsayin shugabanmu Manzon Allah (SAW) ba?

Wadannan Allah zai yi musu kamun ramuwa, domin Ya ce a cikin LittafinSa: “Kuma Allah Yana tsare ka daga mutane.” (K:5:67). Utbah dan Abu Lahabi ya cutar da shi ya yi masa isgili, sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka shushuta masa wani kare daga cikin karnukanKa.” Sai ya zamo bai iya barci sai a tsakiyar ’yan uwansa saboda tsoron addu’ar Manzon Allah (SAW), amma wannan bai kare shi ba, domin a daya daga cikin tafiye-tafiyensa sai ya farka ya ga mafadacin zaki ya sanya faratunsa a muka-mukinsa, sai ya fasa ihu yana cewa: “Ya ku mutanena! Addu’ar Muhammad ta kashe ni.” Kuma wannan bai wadatar da shi da komai ba.

Kisra ya keta wasikarsa sai ya yi masa addu’a, sai Allah Ya hallaka shi a zamaninsa, Ya kekketa mulkinsa kekketawa, mulki bai sake komawa hannun Kisrawa ba a bayansa, domin tabbatar fadinSa Madaukaki: “Lallai mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.” (K:108:3).  Domin haka duk wanda ya zage shi ko ya tozarta shi ko ya nakasa shi ko ya yi gaba da shi, to lallai Allah zai karya kashin bayansa Ya debe albarka a idonsa da zuriyarsa. Ya zo a cikin Sahihu daga Annabi (SAW) cewa lallai ya ce: “Allah Madaukaki Yana cewa, duk wanda ya yi adawa da wani waliyiNa, hakika Na yi masa izini da fafata yaki da Ni.” To yaya kuma wanda ya yi adawa da Shugaban Annabawa (AS)?

Allah Ma’abucin Tsarki Yana cewa: “Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.” (K:15:95). Kan tafsirin wannan aya Ibn Sa’ad (Rahimahullah) ya ce: “Hakika Allah Ya aikata haka, babu wanda ya bayyana isgili ga Manzon Allah (SAW) da abin da ya zo da shi face Allah Ya hallaka shi, Ya kashe shi mugun kisa.” Sannan Dabarani a cikin Al-Ausad da Baihaki da Abu Nu’aim su biyun a cikin Ad-Dala’il da Ibn Madawiyya da sanadi mai kyau da Ad-Diya’u a cikin Almukhtarat sun ruwaito daga Ibn Abbas (RA) kan fadinSa Madaukaki: “Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.” Ya ce: “Masu isgilin su ne Walid bin Al-Mugira da Al-Aswad bin Abdu Yagusa da Al-Aswad bin Mudallib da Alharis bin Andalus Sahmiy da Al-As bin Wa’il….”

Karashen Hadisin ya nuna dukansu Allah Ya hallaka su daidai-da-daidai da cututtuka daban-daban, wadansu daga cikinsu ma ba a garuruwansu ba (Haka lamarin zai kasance ga wadanda suka cutar da shi a bayansa).