✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada mu raina alheri a rayuwa

Tare da sallama, kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. A wannan makon kuma, za mu duba muhimmancin da ke tattare da yin alheri da kuma…

Tare da sallama, kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. A wannan makon kuma, za mu duba muhimmancin da ke tattare da yin alheri da kuma kula da shi komai kankantarsa. Kada mu mance da cewa, masu iya magana sun ce, alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza. Wannan magana karfe ce, domin kuwa babu ko tantama, alheri ba ya zama cuta, sai ma dai ya zama magani. Ba magani kadai ba, alheri kan zama maganin magunguna. Watau mai maganin masifu da cututtuka masu yawa ga dan Adam. Bisa ga wannan batu, bari mu duba wani labari, wanda ya faru a zahiri, watau ba kirkirarre ba ne.
Wani bawan Allah ne yake tafiya da motarsa, ya nufi Kaduna daga Zariya. Yana cikin tafiya, ya kawo cikin Kaduna, ya zo daidai bakin wata makaranta, sai ya ga wasu dalibai suna tsaye bakin hanya, sai gumi suke yi. Ga yadda alama ta nuna, sun dade suna jiran mota, amma ba su samu ba, domin kuwa lokacin da aka tashi daga makaranta ya dan yi nisa sosai. daliban nan suna ganinsa, sai suka tsayar da shi. Kamar ba zai tsaya ba, sai dai wata zuciya ta gaya masa cewa ya kamata ya tsaya.
Da mutumin nan ya tsaya, sai suka roke shi da cewa, don Allah Ya taimaka musu, motar da ke daukar su daga makaranta zuwa gida ce ta lalace, don haka a cikin ta haya suka zo makaranta, kuma ga shi tun dazu aka tashi, amma ba su samu wacce za ta kai su gida ba. Da mutumin nan ya tambaye su unguwar da za su, sai aka yi katarin cewa, ta hanyar unguwar ma zai bi. Bisa ga haka, sai ya dauke su, ya kai su har gida.
Da daliban nan suka sauka daga motar, sai suka tambaye shi cewa, nawa ne za su biya, shi kuwa ya ce ba zai amshi kom kwabo nasu ba, ya dai taimaka masu ne. Suka yi ta godiya tare da yi masa addu’a mai ratsa zuciya. Shi kuwa ya kama gabansa, yana mai jin dadi a ransa.
Dayake sai da ya kai kusan mako daya a Kaduna, watau wata hidima ya je yai, don haka bai koma gida Zariya ba sai bayan kamar mako daya. Ranar da ya koma gida, ya zauna ke nan, ’ya’yansa sun zo suna gaishe shi, sai daya daga cikin ’ya’yan nasa, wata yarinya mai wayau ta fara ba shi wani labari.
“Baba, kwanaki mun sha bakar wahala a hanya, lokacin da muke dawowa daga makaranta.” Inji yarinyar.
“Assha! Me kuma ya faru da ku a hanya? Inji dai ba hadari kuka yi ba a motar!” Ya tambaye ta cikin damuwa a tare da shi.
Ita kuwa yarinya sai ta ce: “A’a baba, ba hadari muka yi ba. Bayan mun taso daga makaranta, direbanmu ya zo ya dauke mu, kawai sai motar ta lalace a hanya. Muka yi ta turi har muka gaji, amma motar nan ba ta tashi ba. Ganin haka ya sanya muka tsayar da wani mai mota, muka roke shi ya dauke mu. Ya kawo mu har gida, kuma bai amshi ko kwabo ba. Wallahi da ba domin mutumin nan ba, da sai mun kai dare ba mu koma gida ba, domin babu motocin haya a kan titin.”
Jin wannan batu na diyarsa, mutumin nan sai ya yi kasake, ya shiga tunani. Sannan ya tambayi yarinyar daidai ranar da al’amarin ya faru, sai ta ce masa ai a ranar da ya tafi Kaduna ne al’amarin ya faru. Allah mai yadda Ya so! Da ya yi kintace da lissafi, sai ma ya gano cewa, kusan duk lokaci daya ne da lokacin da ya taimaki ’yan makarantar nan.
Wannan labari na kara tabbatar mana da cewa, lallai alheri danko ne kuma ba ya faduwa kasa banza. Haka kuma ke kara nuna mana cewa, alheri ba ya kadan, komai kankantarsa sunansa alheri, kuma zai iya haifar da sakamako mai kyau ga duk wanda ya aikata shi.
A duk lokacin da ka yi alheri, ka shuka wani tsiro ne mai inganci, wanda ba zai rube ba, zai rayu kuma ya tashi, ya haifar da kyakkyawar yabanyar da Allah Zai ba ta ruwa ta yi girma har ta samar da ’ya’ya masu dadi da gardi, wadanda za su zagayo har zuwa ga kanka da iyalinka, ku sha ku amfana. Don haka, kada mu raina alheri. A lokacin da kake taimakon wani, wani kuma na can yana taimakon naka. A lokacin da ka tausaya wa wani, wani na can yana tausaya wa naka ko kuma yana tausaya wa kai kanka. Idan muka dauki halayyar taimako da yada alheri, babu shakka za mu kasance al’umma mai tallafar juna, mai taimakon juna da cire wa juna takaici.
Mu jaraba wannan halayya ta alheri mu gani, lallai kam ba za mu ga akasi ba, sai dai mu ga alheri. Domin kuwa alheri ba zai taba haihuwar mugunta ba. Allah Ya sanya mu dace, amin!