✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada ku yarda PDP ta dawo mulki – Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya bukaci ’yan Najeriya da kada su kuskura su sake zabar Jam’iyyar PDP a zaben 2019 da…

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya bukaci ’yan Najeriya da kada su kuskura su sake zabar Jam’iyyar PDP a zaben 2019 da ke tafe.

Alhaji Balarabe Musa wanda ya bayyana haka a Kaduna a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Talata ya ce al’amurra za su yi kara tabarbarewa in har aka yarda Jam’iyyar PDP ta sake dawowa karagar mulkin kasar nan.

Ya ce Jami’yyar PDP ta yi mulki na tsawon shekara 16 kafin zuwan wannan gwamnati a shekarar 2015, “Babu abin da suka kawo a kasar nan face talauci da rashin ci gaba.” Ya kara da cewa, Jam’iyyar PDP ta yi kusan durkusar da kasar nan baki daya ta hanyar cin hanci da rashawa da almubazzaranci da kudaden jama’a a yayin da take kan karagar mulki.

Tsohon Gwamnan ya ce, duk da cewa, al’amura ba su gyaru yadda ya kamata ba a karkashi gwamnatin APC, bai kamata al’ummar Najeriya su yi tunanin cewa PDP za ta gyara wani abu a kasar nan ba. Ya ce, Jam’iyyar PDP ba ta da mutuncin sake dawowa karagar mulki. A kan haka ya bukaci a sake nemo wadansu masu mutunci da za a damka wa mulkin kasar nan wadanda za su kawo gagarumin canjin da ake bukata.”

“Babu wani dalilin da PDP za ta sake neman sake dawowa karagar mulkin kasar nan, ban fahimci dalilinsu ba, su dawo su yi me? Jam’iyyar ce ta haifar da dukan matsalolin da ake fuskanta a tsawon shekara 16 da suka yi suna mulki, wannan ba zai yiwu ba. Tabbas abubuwa ba sa tafiya daidai a kasar nan a yanzu, amma ina tsammanin lamurra za su kara lalacewa idan har aka bar PDP ta sake dawowa karagar mulki.

“Bai kamata ’yan Najeriya su amince da Jam’iyyar PDP ba sam, abin da muke bukata a yanzu shi ne wadansu ’yan siyasa na daban wadanda za su samar wa kasar nan mulki nagari da jama’a ke muradi tsawon lokaci,” inji shi

Ya koka kan yadda a ’yan shekarun nan kudi ya yi tasiri a siyasar kasar nan abin da ya yi sanadiyyar fitowar ’yan siyasar da ba su da farin jini a wajen jama’a.