Hajiya Amina Abdullahi wacce ake kira da Kaduna tsohuwar ma’aikaciya ce da ta yi ayyuka da dama tun a tsohuwar Jihar Kaduna zuwa Jihar Katsina kafin ta koma Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) inda ta yi ritaya a matsayin Babbar Manajar Rukunonin Kamfanin (GGM). A hirarta da Aminiya ta bayyana gwagwarmayar da ta sha da kuma shawararta ga mata:
Tarihina
Sunana Hajiya Amina Abdullahi, amma da sunan mahaifin kuma sunana Hajiya Amina Sa’idu Labo DO, wacce aka fi sani da suna Kaduna. An haife ni a Unguwar Rafindadi a Katsina ranar 24 ga Oktoban 1955. Amma a shekarar da aka haife ni aka mayar da mahaifina Kaduna da aiki a karkashin Gwamnatin Arewa ta wancan lokaci, wannnan shi ne dalilin da ya sanya aka fi kirana da Kaduna. mahaifina Sa’idu Labo shi ne DO bakar fata na farko da aka nada bayan tafiyar Turawan mulkin mallaka.
Na yi makarantar firamare a LEA Doka a Kaduna daga nan na wuce makarantar ’yan mata ta Tarayya ta Ilorin wato Kueen Elizebeth inda na kammala karatun sakandare dina. Sannan na je Makarantar Share Fagen Shiga Jami’a (SBS) da yake ina fannin kimiyyya ne daga nan kuma sai na yi digiri a kan Kimiyyar Zanen Gine-Gine (Architecture), kuma ina shekarar farko ta karatun digirina yi aure, kafin in kammala a 1979 sai da na haifi ’ya’yana biyu Zainab da Fatima.
Aiki
Bayan na kammala digiri sai na fara aiki a Hukumar Gidaje ta Jihar Kaduna wato Kaduna daga bisani aka mayar da ni KASUPDA da aiki. Nan na yi ta aiki har sai da aka kirkiro Jihar Katsina a 1987.
Bayan da aka mayar da duk ma’aikata ’yan asalin Jihar Katsina zuwa Katsina da aiki, ni ce ta farko da ka ba wa Hukumar Gidaje ta Jihar Katsina. Daga nan kuma na zama Babbar Sakatariya ta Ma’ikatar Ayyuka ta Jihar Katsina daga nan da Alhaji Sa’idu Barda ya zama Gwamna sai ya mayar da ni Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Kasa da Safiyo ta Jihar Katsina. Ina nan sai Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya aiko yana neman ’yan asalin Jihar Katsina wadanda suka karantar Kimiyyar Zanen Gine-Gine, to sai aka bada sunana. Na tafi Legas suka yi mini jarrabawa biyu da kuma intabiyu biyu a karshe na ci suka dauke ni aiki cikin taimako Allah.
A 1983 sai aka mayar da aikina daga daga Jihar Katsina zuwa NNPC. Na fara aiki a NNPC a matsayin Manaja, har na kai Janar Manaja inda daga karshe na yi ritaya shekara biyar da suka gabata 2015 a matsayi GGM a NNPC.
Nasarori
Na farko zan fara da cewa alhamdulillah, na gode Allah da Ya ba ni damar yin duk abubuwan da na yi, sannan tilas in gode wa mijina Allah Ya jikansa, wanda duk irin ayyukan da na yi, na samu nasarar yin su ne ta hanyar goyon baya da tallafin da na samu daga gare shi. Sannan babbar nasara ita ce gamawa da mutane lafiya tun daga lokacin da na fara aiki har lokacin da na gama. Musamman a NNPC din nan inda ka san wuri ne mai muhimmanci. Amma cikin ikon Allah ga shi na gama lafiya ba tare da an tuhume ni da wani laifi ba.
A ina kika hadu da mai gidanki ?
Mun hadu da shi ne a Kaduna a lokacin yana tukin jirgin sama, ni kuma ina sakandare amma ba mu yi aure ba har sai da na shiga shekara ta daya a jami’a.
Wane hali kika fi so game da shi ?
Halin da na fi so game da shi shi ne fahimta. Mun fahimci juna sosai, musamman ganin cewa aikina a NNPC aiki ne mai sanya yawan tafiye-tafiye. Don na zagaya duniya amma kuma da yake ya fahimce ni kuma ya yarda da ni ya san cewa ba zan taba yin wani abu da zai bata masa suna ba, ya amince mini bai taba zargin wani abu ba.
Yaya kike ji a matsayinki na mahaifiya?
Alhamdulilllahi babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah da Ya bani zuriya kuma Ya shirya mini su ba sa tayar mini hankali. Wadanda suka yi aure suna zaune da iyalansu lafiya haka wadanda ba su yi ba suna yi mana biyayya kuma ina yi musu addu’ar Allah Ya ba su maza nagari. Wannan shi ne babban abin da nake jin dadi.
’Ya’ya nawa kike da su?
Ina da ’yaya biyar mata hudu da namiji daya da kuma jikoki goma.
Kalubale
Akwai kalubale da dama misali akwai maganar cika alkawari da kuma yin adalci. Ka ga yanzu kamar maganar rushe kananan shaguna na Kasuwar Kaduna da muka gina a farkon aikina a Kaduna, dama can asali a takardun duk wanda aka ba shago a wannan kasuwa ta Santara ta Kaduna an rubuta a kan takardar cewa wannan wuri ba wauri ne na dindindin ba. Sannan wurin na gwamnati ne kuma gwamnatin tana da damar ta karbe wurin a duk lokacin da ta ga dama ba tare da ta biya diyya ko ta sisin kwabo ba, amma ka ga yanzu mutane suna ta zagin Gwamna El-Rufa’i kan cewa wai zai rushe kasuwa a kan zalunci. Wannan yana nuna cewa masu wannan magana da suke zarginmu, mu da muka gina kasuwar da cewa mun cuce su ba su da ma asalin wannan takarda ta mallakar shagunan. Sannan ka ga na yi aiki da gwamnonin soja da dama wannan ma wata dama ce daban tunda ka san aiki da soja ba karamin abu ba ne. Don haka mun fuskanci kalubale da dama a rayuwa amma dai mun gode Allah na Ya ba mu damar ganin bayansu lafiya.
Me kike fata a rayuwarki a nan gaba?
Ina fatan in ga mata sun inganta dangantakarsu a tsakaninsu da iyalansu. Mata su sani cewa ya kamata su mayar da hankalinsu ga iyalinsu da farko. Duk irin aikin da suke yi kada ya kawar da su daga kula da mazansu da ’ya’yansu. Mata su daina barin tarbiyyar ’ya’yansu ga masu yi musu aiki a gida domin wannan ne zai sanya karsashin soyayyar uwa da ’ya’yanta ya ragu.
Domin ni ko a lokacin da muka tashi muna yara ba mu san lokacin da iyayenmu mata suke kwanciya ba, kuma ba mu san lokacin da suke tashi daga barci ba. Don a duk lokacin da za mu kwanta barci za ka iske su suna tsaye ne suna yin wani aiki haka kuma duk safiya ta Allah su ne suke tayar da mu.
Wace shawara mahaifiyarki ta taba ba ki da ba za ki manta ba?
Shawarar da take ba ni a koyaushe ita ce ta kula da addinina. Sannan ka ga dai da farko mahaifina a koyaushe yakan ce kada ku yi wasa da sallolinku kuma ku kula da rufe kanku idan magariba ta yi, domin duk wani abu da kuka ga addini ya hana yana da dalili. To a lokacin sai dai mu amsa mu ce to Baba, ba mu taba tambayar dalilin haka ba saboda kunya. Ba kamar yanzu ba, saboda idan yanzu ne ka fada wa danka kada ka yi kaza sai ya tambaye ka me ya sanya saboda yanzu komai suna son su sani.
Wane tufafi kika fi so ?
In dai fita zan yi na fi son in sanya doguwar riga baka.
Ganin yawan shekaru da kike da su idan mutum ya kalle ki sai ya ga har yanzu kina da sauran karfi mene ne sirrrin?
Babu wani wani sirri da ya wuce wadatar zuci, ba wai maganar cin abinci mai kyau ba ne ko wani abu daban.
Ko kina cikin wasu kungiyoyi da kike aiki a yanzu ?
Eh, ko yanzu ina aiki, akwai wani tsohon shugabana da muka yi aiki da shi a NNPC wato Alhaji Aminu Baba Kusa, wanda shi ne jagoran wata gidauniya ta kasa da kasa da take da Masallacin Annur na nan Abuja. To bayan na yi ritaya sai ya tambaye ni ko ina son zan yi aiki sanin cewa na saba da aiki bana iya zama haka. Na amsa masa cewa ina son yin aiki, don haka ya ba ni aiki a wannan wuri yanzu ni ce Daraktar Ayyukan Jinkai a wannan wuri. Muna gabatar da ayyukan ciyarwa a wurin da watan azumi da kuma wasu ayyuka na lafiya a karkara.
Yaya kike yin hutu?
Yadda nake hutawa, shi ne ka san a da lokacin da nake NNPC tun karfe takwas nake fita aiki kuma wani lokaci ba na dawowa gida sai wajen karfe 10, amma yanzu kuma sai bayan karfe 11 nake zuwa aiki, don haka zan ce yanzu ina hutawa sosai.
Wadanne kasashe kika ziyarta?
Kusan in ce ba zan iya lissafa kasashen da na je ba, amma dai zan ce na je Saudiyya sau da dama na je Dubai na je Amurka ba iyaka na je Japan kai kusan dai in ce Nahiyar Austireliya ce kawai ban je ba.
Wace kasa ce ta fi baki sha’awa ?
A gaskiya duk a cikin yawon da na yi kasar Saudiyya ita ce ta fi burge ni kuma abin da ya fi ba ni sha’awa game da ita shi ne yadda ake ginin fadada Masallacin Makka. A gaskiya akwai abin sha’awa da al’ajabi game da wannan aiki musamman da yake ni na karanta fannin zanen gini ne. sannan idan ka kalli yadda aka gina ’Zam-Zam Tower’ da ’Clock Tower’ za ka san an yi amfani da kwakwalwa sosai.
Daga nan sai kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), abin da ya fi ba ni shawa’a da daukar hankalina a can shi ne dogon ginin nan da ya fi kowane gini tsawo a duniya. Na shige shi a lokacin ana yin sa. Ba zan manta ba mun je ne tare da tsohon Shugaban NNPC na Kasa Barkindo Mustapha. Saboda tsayin gini idan ka shiga lifta za ta kai ka kamar hawa na 50 sannan sai ka sake canJa wata liftar ita ma ta kai ka misalin hawa na 100 sannan kuma ka canja wata, kuma kowane hawa akwai masallaci. Da yake sun yi mini bayani, ni a matsayina na mai zanen gini na fahimci irin fasahar da suka yi amfani da ita tana da ban sha’awa sosai. Muna cikin irin wannan kololuwa ne sai Barkindo ya leka kasa, sannan ya ce mini Hajiya leka ki gani. Bayan na leka sai ya ce da ni “yanzu Hajiya idan muka mutu a wannan wuri yaya za mu ce? Anya ba ganganci ba ne, gara mu sauka mu kyale Larabawan nan da kasadarsu.” Haka muka sauko. To ka ga wannan gini shi ma akwai abin sha’awa a cikinsa sosai.
Wani abu kuma da ya kara burge ni shi ne wani jirgin kasa mai gudun gaske irin mai tafiya a karkashin kasar nan, da na taba hawa a Japan. Nisan inda za mu je ya kai daga Legas zuwa Maiduguri amma kwata-kwata ba mu wuce minti 30 ba ya kai mu ya ajiye. Wannan ma abu ne mai ban al’ajabi sosai.
Tunda yake kin ga jiya kin ga yau, yaya za ki kwatanta yadda hulda take tsakann shekarun baya da kuma yanzu?
A gaskiya ba za a hada yadda yanayin zamantakewa yake ba a da da kuma yanzu. Ka ga a da akwai aminci da yarda da kuma gaskiya a tsakanin jama’a. Misali a lokacin da muka tashi muna yara a Kaduna za ka ga babu katanga a tsakanin gidajenmu. Don haka yara makwabta duk tare muke wasa da sauran lamura kamar yadda su ma iyayenmu suke tare. Domin iyayenmu idan sun dawo aiki a wuri daya suke taruwa bayan sun yi Sallar Isha’i su ci abinci tare. Sannan mu ’ya’yansu mun san a cikin iyayen nan namu akwai mai bulala akwai mai fada kuma mun san wanda ko da ma laifi muka yi za a doke mu za mu ruga wurinsa don mun san ba zai bari a buge mu ba. Kuma idan ka yi laifi ka san baban abokinka ko kawarki zai iya zane ki ba ma za ka iya zuwa ka fada a gida ba don ka san kara maka za a yi.
Sannan koda a tsakanin masu aikin gida za ka iske akwai wannan yarda da amana. Misali ni tun a wancan lokaci da na tashi na samu gidanmu akwai mota, saboda mahaifina D.O ne kamar yadda na fada maka. Saboda haka akan sanya direba ya dauke mu daga Kaduna zuwa Katsina ba tare da fargabar cewa zai ci zarafinmu ba ta hanyar yaudara ko fyade ko wani abu makamancin haka. Ba kamar yanzu ba inda ko makaranta za ka sanya direba ya kai yaranka sai kana yin taka-tsantsan don kada shi da kansa ya yi musu fyade ko kuma ya kai su wajen da za a yi musu ko ma a hada baki da shi wajen yin garkuwa da su.
Sannan wani muhimmin abu da ya kamata mata su sani shi ne wajen tarbiyya da ba da ilimi ya kamata su daina nuna bambanci a tsakanin ’ya’ya maza da mata. Domin ni na yarda cewa a komai Allah Ya bambanta maza da mata, Ya ba wa kowannensu irin darajarsa ta bangaren abin da zai iya yi. Kai ko ta bangaren halitta ma haka abin yake. Amma wuri daya ne Allah bai sanya wannan bambanci ba, wato wurin kwakwalwa da kuma abin da kwakwalwar take iya yi na ilimi.
Misali idan aka samu wani namiji yana aiki ko dabi’a irin ta mata za ka ji an ce yana kwaikwayon mata haka idan aka samu mace tana yin ayyuka irin na maza za ka ji an ce tana yi kamar namiji. Amma ba za ka taba jin haka ba idan abin ya zo ta fannin ilimi. Ba za ka ji an ce wannan yarinyar tana da ilimi kamar namiji ba.
Shawara ga mata
Kamar yadda na fada a baya, ya kamata mata su kula da ilimin ’ya’yansu da tarbiyarsu. Sannan su kara kyautata wa mazansu.