Daniel Akpeyi golan da ya kama wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kwallo a Gasar Cin Kofin Afirka a Masar, ya ce bai dace a kori Gernot Rohr daga aiki a wannan lokaci ba.
Akpeyi wanda da yawa daga cikin magoya bayan Super Eagles ba su gamsu da yadda ya yi wa Najeriya gola a yayin gasar ba, ya ce masu kiraye-kirayen a kori kocin a wannan lokaci ba su yi masa adalci ba kuma ba ’yan kasa nagari ba ne.
“A gaskiya kocin ya yi kokari musamman ganin yadda ya kai Najeriya mataki na uku a gasar. Sannan shi ya kai Najeriya Gasar Cin Kofin Duniya a bara,” inji shi.
Idan za a tuna jim kaxan bayan Aljeriya ta lallasa Najeriya a wasan kusa da na karshe waxansu suka rika kiran a kori Gernot Rohr.
Sai dai alamu sun nuna da wuya a kori kocin, ganin yadda Hukumar NFF ta ce tana goyon gayansa.