Tsohon Mataimakin Sakataren jam’iyyar APC na Kasa, Timi Frank, ya yi raddi ga kalaman Ministan Shari’a, Abubakar Malami, game asalin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.
Malami ya bukaci wata kotun tarayya ta hana Atiku yin takara saboda ba dan asalin Najeriya ba ne.
- An fara farautar ’yan bindigar da suka kashe ’yan sanda a Taraba
- Osinbajo ya daura wa Usman Alkali Baba sabon mukaminsa
- Sojoji sun bayyana sunayen daliban Kwalejin Kaduna da aka kubutar
- Dalibai biyar na Kwalejin Harkokin Noma ta Kaduna sun kubuta
Timi Frank, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce “Kamata ya yi ka maida hankali wajen warware matsalolin Najeriya ba neman asalin Atiku ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Atiku dan asalin Najeriya ne, wanda ya yi gwagwarmaya ciyar da dimokuradiyya da tattalin arzikinta gaba.
“Abun takaici ne fitowar wadannan soki-burutsu daga bakin mutum kamar Malami, musamman a wannan yanayi da kasa ke ciki.
“Irin wadannan kalamai ne suke haddasa rarrabuwar kai da fitina a tsakanin mutane.
“Ta yaya Malami zai ce Atiku ba dan Najeriya ba ne? Mutumin da ya taba yin takarar gwamna a Jihar Adamawa kuma ya ci, sannan ya yi Mataimakin Shugaban Kasa har na shekara takwas.
“Yaya za a yi a mutumin da ya taba aiki a Hukumar Hana Fasa Kauri ta Kasa, ya yi wa kasa hidima, a ce ba dan kasa ba ne?
“Wannan ba komai ba ne face wata siyasa wadda za a yi amfani da ita wajen bata sunan mutum mai nagarta kamar Atiku,” a cewar sa.