Wata babbar kotu a kasar Burkina Faso ta dage sauraron shari’ar mutanen da suka kashe jagoran juyin-juya halin kasar, Thomas Sankara, wanda aka kashe a 1987.
Iyalan jagoran ne suka bukaci a dage zaman kotun da ake yi har zuwa lokacin da al’amura suka daidaita kasar, sakamon yanayin da kasar ta shiga bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yi.
- Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘farfaganda’
- NAJERIYA A YAU: Ka’idojin tuki da mutane suka dauka kwalliya ce
Iyalan Thomas Sankara sun bukaci hakan ne saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo, inda suka ce suna so a ci gaba da shari’ar da zarar an dawo da bin tsarin mulkin kasar.
Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta dakatar da Burkina Faso daga cikinta a ranar Litinin, kwana uku ke nan bayan ita ma Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da kasar.
Tawagar hadin gwiwa ta Majalisar Dinkin Duniya da ECOWAS da ke Ouagadougou, babban birnin Burkisa Faso, na tattaunawa da sabbin shugabannin mulkin soji na kasar.
Tuni sauran manyan kasashen duniya da kungiyoyi suke ta kokarin sulhunta tsakanin dakarun sojin da suka hambarar da gwamnatin farar hular kasar, domin ganin sun mayar da mulki ga farar hula.