Haurobiyawa Kukan Tenhiya ya karu a Arewacin asar nan, domin kullum sai kisan mummuke da na kiyashi ake yi wa al’umma; wasu kuwa an tursasa su sun arce zuwa wuraren da ba su taba zuwa ba. Kuma babban abin takaicin shi ne, a kowane fanni na rayuwar al’umma Shagabanni sun juya wa al’umma baya. Ga dai ciwon cabin –boko, wanda a da na dauka akwai kwararrun bokayen Turai da suka dukufa wajn magance shi, amma har yanzu shiru ake ji, wai Malam ya ci shirwa.
’Yan makarantar Dodorido, da a jihohin Bararon-nono da Yawon Bebe kawai muke samun labarin yamutsin haramta bobo da kwambon bokoko, amma yanzu bayan ya mamaye su Alan-guburo da jama’ar babban birnin Dama-tumatur, sai ya haura cikin Jihar da Fullo ke damawa. Kai Arewatawan Haurobiya sun ga tasku.
Masu yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, sun sha furta cewa, “mai turaka shi yasan inda take yoyo,” amma yanzu wannan al’amari ya sauya. Domin sanin kowa ne a fadin Arewacin Haurobiya da zarar rmutum ya hango inda turakarsa ko shigifarsa ke yoyo a lokacin marka-maraka, ko ya toshe, sai wta bular ta kunno kai.
Lallai lokaci ya yi da Haurobiyan da ke cikin jam’iyya mai dan botoda sanda jirge, su sani cewa a gaban na-mujiyarsu ake yi wa fullo awon gaba da karsana da nagge, sannan aka bi shi da bita da kulli, inda duk rikicin da ya auku a wasu sassan na Arewacin Haurobiya sai a dauki alhakin fullo. Kai saboda musgunawa fullo da ake yi, har ta kai ga Gwamna Gwaramgwam, Sususun-wawan Makurda ya ziyarci fadar Shugaban kasar Haurobiya, ya kuma bijiro da bukatar ganin lallai an kori fullo daga fadin Haurobiya.
’Yan dugwi-dugwi da masu koyon watsattsake dabuda wagagen littattafai su ma ba su tsiraba, domin an sha kai musu farmaki, sannan ga tsallen badaken direbobin alli da jami’an asusun ilimi, wadanda ke fafutikar a kara musu ladar kwadago, kodayake akwai masu hankoron ganin an samar da kayan inganta tukin alli a kowane mataki na yaki da juhala, don tabatar da adala.
A daidai lokacin da nike kattaba muku darasin wannan mako, na samu bayanan da suka tabbatar da cewa Barden Bade, babban barden burgar gadin Haurobiya,ya kwashe iyalansa daga garin Mun-bi, tun kafin masu yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko su far wa garin; su kuwa gama-garin al’umma ya wancakalar da su, ko oho!
A daidai lokacin da Haurobiyawa ke jimami da alhinin a jihonin Gabashin Arewacin Haurobiya, sai ga iyayen al’umma ko in ce Dattabai daga yankin, wadanda suka hada da Dumu Wakilin Dumawa da Dumu-Dumu Muzu-Muzu, shugaban Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge sun yi cincirindo a dandalin mikiya, suna ta kwarzanta Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulkin mulaka’u. a hangoronsa na yin tazarce a karo na karamin lauje. Wadannan miyagun Dattabai, hakika sun tabe, domin tabararsu tana cike da waskiya, inda suka yi wa al’umma zuki-ta-malle kama kare ka hada shi da zomo.
Batu na ingarman karfen karafa, lallai mudukufa wajen ganin mun wancakalar da jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, kuma kada mu yi saurin bai wa ’yan adawa damar yi mana damo-da-kura-da-diya, har sai mun kulla yarjejeniya da su game da salon jagoranci da kyautata rayuwar al’umma, ta yadda idan mutum ya saki tafarki,sandar mu na nan, sai kawai mu rafko shi. Domin mun dade da sanin cewa,’adawa in babu dawa, sai a shiga dawa!”
A daidai wannan bagire, ina mai gargadin Dauda-mai-maki da Tumbin-wulli, su daina bari ana keta doka, wajen aiwatar da tsare-tsaren kasa,musamman ma yadda ake yin TUWONA MAINA a tsakanin ‘’yan Hauren-Danja, wadanda ke ikrarin dan uwansu ne a kan karaga,kuma idan aka hana shi yin tazarce, su za su daura yaki da kasarsu ta haihuwa. Kowa dai ya san Asararren Dokin-bobo ko in ce Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku.
Haurobiyawa na sanin kullum a kwai managartan mutane da ke laluben mafita daga mawuyacin halin da kasar nan ta tsinci kanta a ciki, amma al’amari mafi a’ala da ake ta yawan kwakwazonsa, shi ne mu yi ta rokon Mai-duka, don ko mun samu saukin dukan da muke sha. Hakika ina da tabbaci cewa Mai-kowa, Mai-komai zai iya samar mana da mafita cikin kankanen lokaci, amma ya zama dole mu yi Na-jaki, don kar mu ci Na-jaki; ban da Juyin wainar matar matar mai san’ar na duke.
A gurguje, a gurguje, idan ba mu kakaba wa kawunanmu tagiyar Malam Mantau ba, za mu iya fasko yadda wani mai sana’ar na-duke ya jefa tsohon auransa cikin wata tsohuwar kwakware, sannan ya nemi a taimaka masa a cike kwakwaren da kasa, amma duk sa’adda aka tula kasaa ciki, sai aura yayi karaji, sannan ya daka tsalle ya dare bisa kan tarin kasar. Don haka daidailokacin da kwakware ta cika sai aura ya taka sama ya fito waje, wato dai iya gani, iya kyalewa.
Ita kuwa mai dakin nomau na manomi, idan har kun kakaba wa kawunanku taguiyar Malam Tunau za ku fasko yadda ta yi wa maigidanta isgili kan lallai ya kwance igiyar turken rayuwarsu, domin ita idan ta juya sai a ji ta a gidan hamshaki wane. Wannan mashahurin batu ne, da shi da na nomau mai tsohon aura, duk mun taba bijiro muku da su a farfajiyar wannan makarantar; kuma ina kyautata zaton duk mun yi darasinsu ne cikin shekara ta dubu karamin lauje da kwanciyar magirbi.
Babbar mafita dai a garemu, ita ce kyautata dabi’unmu, wanda duk bay a son a musguna masa, o kada ya musguna wa wani; wanda duk ya kauce wa alkawarin kanzon kurege,to magaftansa ba za su samu nasara a kansa ba. To kun ga ken an idan muka ci gaba da bai wa miyagu dama suna ja mana ragama,tamkar kulla wa kawunanmu makirci muke yi, shi ya sama idan mun roki Mai-duka, sai mu ji kamar ya yi biris da mu. Da wannan nike ganin mu za mu yunkurin rage Kukan Tenhiyarmu, ta hanyar JUYIN AYA, TAKANdA! Mu dai ba wasan adon gari muke yi ba, ko kuma tsalle-tsallen dandali’yan lalle. Masu yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-insa-ba, sun ce ‘Kukan Kurciya Jawabi ne, mai hankali yake ganewa. Ni kuwa na ce “Kukan Tenhiya Bayani ne, Haurobiyawa kadai ke ganewa.’