✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ne zai jagoranci Kiristoci masu ziyarar ibada a bana – Okparah

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne zai jagoranci Kiristoci zuwa ziyarar bauta a Urshalima a bana.Babban Sakataren Hukumar Kula da Kiristoci masu Ziyara ta kasa…

Shugaban Kasa Dokta Goodluck JonathanShugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne zai jagoranci Kiristoci zuwa ziyarar bauta a Urshalima a bana.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Kiristoci masu Ziyara ta kasa (NCPC) Mista John Kennedy Okprah, ne ya bayyana haka a Gombe lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, a gidan gwamnati a ranar Talatar da ta gabata.
Mista Kennedy, ya yaba wa Gwamna dankwambo kasancewarsa Gwamna na farko da ya fara amincewa Mataimakinsa ya shiga tawagar Shugaban kasar don zuwa a yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya a lokacin ziyarar a wajen Najeriya.
A cewarsa ganin cewa addu’a ita ce ginshikin zaman lafiya ya sa Hukumar NCPC ta yi shirin bullo da wani shiri ga mabiya addinin Kirista da zai sa su rikaa daukar ’ya’yansu suna gudanar da addu’o’i tare kamar yadda Musulmi ke zuwa da ’ya’yansu masallatai suna yi.
Ya ce a wannan karo idan lokacin tafiya ziyarar kasar Jerussalam ya yi, Shugaba Goodluck da kansa zai jagoranci tawagar Kiristoci don zuwa ziyarar da yake a bana ziyarar ta musamman ce don yi wa kasa addu’a.
Sai ya roki Gwamnan ya taimaka wajen daukar nauyin mabiya addinin Kirista don su iya zuwa ziyarar Jerussalam. Ya ce a bana an ba Jihar Gombe kujera 400 maimakon kujera 256 da ta samu bara.
Da yake maida jawabi Gwamna Ibrahim dankwambo, ya ce ba zuwa ziyara Jerussalam ne abin burgewa ba kyautata mu’amala da juna ne abin lura.
Gwamna dankwambo, ya ce Musulmi ma suna zuwa Jerussalam saboda masallaci na uku mafi daraja a
duniya wato Masallacin Aksa yana can.
Ya ce zai sa idon don ganin mukarraban gwamnatinsa sun fara daukar nauyin masu zuwa ziyarar da kuma aikin Hajji.
“Ban ce dole ba, amma zan sa ido in ga ko za su iya, saboda na san duk wanda wani ya biya masa kujerar aikin Hajji ko zuwa Jerussalam zai gaya min don in ga wanda ya biya masa din ya kyauta,” inji shi.