✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan da masu yakin neman zabensa a 2015

A makon da ya wuce, Shugaba Goodluck Jonathan ya ba da umarnin a cire ‘allunan cin mutunci da aka kafa a wuraren kawa da ke…

A makon da ya wuce, Shugaba Goodluck Jonathan ya ba da umarnin a cire ‘allunan cin mutunci da aka kafa a wuraren kawa da ke manyan biranen kasar nan, wadanda ke dauke da tallar yakin neman zabensa a shekara ta 2015. Umarnin Shugaban kasar na kunshe ne a wata takarda da mai magana  da yawunsa, Dokta Reuben Abati ya fitar. Ganin cewa Shugaban ya yi matukar damuwa da zabe mai karatowa, hart a kai ga ya yi watsi da hakikanin harkokin mulki, matakin da ya dauka ya zama abin mamaki. Sai dai wannan damuwa ta Jonathan ta auku ne a sanadiyyar ra’ayin da jaridar Washington Post ta buga a kwanaki kadan da suka wuce.
A makalar jaridar Amurka, wadda aka yi wa taken “sakon siyasa mafi muni na shekara, inda aka ragargaji masu yakin neman zaben  Jonathan da suka yi amfani da salon #BringBackOurGoodluck# al’amarin da aka ayyana  da mummunan koyi da abin da ya dauki hankalin duniya kan sakon kiraye-kirayen da ake yi kan a sako ’yan matan Chibock da aka sace daga makarantar sakandaren a Jihar Barno, ranar 15 ga Afrilun 2014.
Saboda toshewar basirarsu ta dukufa kan zabe, Gwamnatin Jonathan ta ki sauraren korafin al’umma gme da rashin cancantar tallafin da take ba su don su tallata takararsa, bisa la’akari da cikin hanci da rashawa a harkokin gwamnati da kuma rashin yin wani kokarin shawo kan kunar bakin wake , al’amarin da ya girgiza kasar nan tamkar yadda aka tafka a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe wata 30, har zuwa karshensa a watan Janairun 1970. A hakikanin gaskiya, Shugaban kasa da kansa, an taba ruwaito shi yana cewa, wannan harin kunar bakin wake ya fi zama barazana ga lafiyar kasar nan fiye da tada kayar bayan ’yan Biyafura.
Abin takaicin, shi ne, kalaman Shugaba Jonathan sun saba wa abin da yake aiwatarwa. A daidai lokacin da ya kakaba wa jihohi uku na Arewa maso Gabas, waddanda rikicin Boko Haram ya dabaibaye su dokar ta baci, abin da ya biyo baya shi ne, tura sojojin da ba su da isassun kayan yaki, duk da dimbin kudin da ake warewa ga harkokin tsaro a kasafin kudi. Sojojin da a nahiyar nan ake takama da su a fagen fama, amma rashin managartan tsare-tsaren jagorancin siyasa ya sa sun fuskanci mummunan kalubale a hannun masu kai hare-haren kunar bakin wake. A irin wannan yanayi na rashin tabbas, sakarkarun masu yakin neman zabe, ba tare da la’akari da mawuyacin halin da kasa ke ciki ba, suna shirya gangami, inda suke ta taka rawa, ba dare, ba rana, su yi ta kai kawo daga birnin wannan jiha zuwa waccan, don jan ra’ayin mutane su yarda cewa Jonathan ne dan takarar shugaban kasa da ya dace a zaba nan da wata shida masu karotowa.
Makonni da dama bayan sace ’yan matan Chibok, gwamnati , wadda ta hada da manyan jami’ai da Shugaban kasa, sun nuna cewa, yaudara ce kawai daga wasu ’yan siyasar Arewa da ke  son yi wa Jonathan zagon kasa a zaben 2015. Bayan da sakon a dawo mana da ’yan matanmu na #BringBackOurGirls” ya dauki hankalin duniya, shugabannin kasa da Firaministoci da shahararrun mutane suka yi ta nuna goyon bayansu a tarukan al’umma, har ta kai ga gwamnati ta fara dan yin wani motsi, inda ta kafa kwamitin da zai binciko gaskiyar lamarin. Tun daga wancan lokacin ake ta jan kafa. Don haka ya kamata a mayar da hankali kan abubuwan da kafafen yada labarai da kungiyoyin fafutikar hakkin al’umma ke bijiro da su, inda ya kamata  ayi la’akari da su, wajen shawo kan matsalar tsaro a kasar nan, ta yadda za a hana satar man fetur a Neja-Dalta da dakile satar dukiyar al’umma da cin hanci da rashawa, don tabbatar da shugabanci nagari, ya kuma ja da baya shirinsa na inganta al’umma, inda ya karke da kyautata wa wasu ’yan tsirari kawai.
Kodayake Shuaban kasar , ta hannun mai magana da yawunsa, ya ce bai damu da abin da ’yan Najeriya ke fada kan inda tsare-tsaren gwamnatinsa ke nufin kai kasar nan. Sai dai ya nuna damuwa kan abin da mutanen kasar waje ke fada, ko suke tunani kan yadda ya dukufa kacokam kan yakin neman zaben 2015. Abati a bayanansa, ya yi nuni da cewa an yi amfani da wadannan alluna ne ba tare da amincewar shugaban kasa ba, ko saninsa ko yardarsa. Wannan lamari na da hadari. kungiyoyin yakin neman zabe suna nan da dadewa, kuma suna da alaka da masu bai wa shugaban kasa shawara. Alamu sun nuna suna samun dimbin kudin da suke biyan kudin tallace-tallace masu tsada a jarida, tare da daukar nauyin shiri a talabijin, kuma suna da jami’an tsaro da ke ba su kariya. Ga shi dai shugabanni sun yi watsi da kukan al’umma a gida, sun kuma yi nazari kan batun muanen waje, wadanda suka yi musu kwakwazo, a nan dai sun yi asara.