✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘‘Jonathan ba zai iya canja wa yarbawa ra’ayinsu kan Buhari ba’’

Kwamitin yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari bangaren ‘Yan Arewa magoya bayan Jam’iyar APC da ke zaune a jihohin kudu maso yamma (Buhari Campaign Organisation…

Kwamitin yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari bangaren ‘Yan Arewa magoya bayan Jam’iyar APC da ke zaune a jihohin kudu maso yamma (Buhari Campaign Organisation Arewa Community South West) ya ce ziyarar kamun kafa da Shugaba Goodluck Jonathan yayi domin ganawa da wadansu sarakuna da dattijan yarbawa a cikin makon jiya, ba za ta canza akalar miliyoyin jama’ar wannan sashe daga kada kuri’unsu ga Janar Muhammadu Buhari a zaben ranar 28 ga watan gobe ba.

“Babu yadda wadannan sarakuna da dattijai da shugabannin kungiyoyi za su iya yi wajen tilasta wa jama’a su canja daga zaben abun da suke so. Yanzu mutane sun waye sun dawo daga rakiyar salon neman kuri’unsu ta hannun sarakuna da ake yi a shekarun baya.”
Jagoran Kwamitin Yakin Neman Zaben Muhammadu Buhari a jihohin yamma, Sarkin Kudun Yamma, Alhaji Hassan Isiaka (JP) shi ne ya fadi haka cikin hira da ‘yan jarida a ranar lahadi a Ibadan.
Ya ce, “jam’iyar PDP ta gane wa idanunta alamomin shan kaye a bayyane daga al’ummar wannan sashe, dalilin firgitar da suka yi ne ya sa Shugaba Jonathan yake yin wannan ziyarar kamun kafa ga Sarakunan wannan sashe wadanda babu abun da za su iya yi wajen bayar da umarni kan abun da ya fi karfinsu. Irin yadda dubunan mutane suka fito a kan tituna suna rera wakokin Sai Buhari, Sai Buhari, a lokacin da Shugaba Jonathan ya kai ziyara zuwa fadar Alaafin na Oyo a ranar Asabar da ta wuce, tabbataciyar shaida ce da ke nuna cewa, al’ummar wannan sashe sun gaji da salon mulkin da ya jefa kasar nan cikin tabarbarewar tsaro da cuwa-cuwa da cin hanci da rashawa da suka haifar da rashin aiki ga miliyoyin matasa.”
Da yake magana a kan matakin yin amfani da motocin kungiyar Direbobi (NURTW) wajen rarraba kayan zabe ga mazabu da Hukumar Zabe (INEC) ta ce za ta yi a ranakun zabe wanda jam’iyun siyasu guda 8 a Jihar Oyo suka ce basu amince da hakan ba kuwa, Sai Alhaji Hassan Isiaka ya yi tambayar cewa, “tsoron me suke yi dangane da wannan muhimmin aiki da INEC ta shirya yi? Wadannan jam’iyu guda 8 da suka fara daukar matakin bijire wa wannan aiki su ne suka fara yin amfani da kungiyar NURTW a shekarun baya wajen tayar da zaune tsaye a sassa daban-daban na Jihar Oyo wanda Gwamna Abiola Ajimobi yayi maganin wannan al’amari. Tun daga lokacin da Gwamna Ajimobi ya kama ragamar mulki shekaru 4 da suka wuce ba a sake jin duriyar rigingimu da ‘ya’yan wannan kungiya suke haddasawa wajen kone-konen kadarori da kashe-kashen rayuka a jihar ba. Bayan rusa kungiyar ta NURTW da Gwamnan ya yi ya zauna da bangarori biyu da suka dade suna jayayya, inda suka fahimci juna kuma suka gudanar da sabon zaben shugabannin reshen kungiyar ba tare da tsoma bakin gwamnati ba, wanda tun daga wancan lokaci ake zaune lafiya a jihar Oyo, sai yanzu ne wadannan jam’iyu suke so su dawo da hannun agogo baya. Ina kira ga Hukumar Zabe ta ci gaba da gudanar da shirin yin amfani da motocin kungiyoyin NURTW wajen rarraba kayan zabe ga mazabu ba tare da sauraren masu neman tayar da kayar baya ba.’’
Shi ma shugaban jam’iyar APC na Jihar Oyo Cif Akin Oke cewa ya yi, ganawa da Sarakunan yarbawa da Shugaba Goodluck Jonathan yake yi domin neman goyon bayan a sake zabensa a zabe mai zuwa ihu ne bayan hari, “domin kashi 80 daga cikin 100 na jama’a da ke zaune a sashen kudu maso yamma sun riga sun yanke shawarar wanda suke so su a zaba, wanda ziyarar Shugaba Jonathan ga Sarakunan ba za ta yi wani tasiri da zai sa jama’a su canza shawarar da suka yanke tun farko ba. Duk wanda yake tunanin ziyarar Shugaba Jonathan za ta iya canza shawarar da jama’a suka riga suka yanke to yana zolayar kansa ne, domin mutane sun gane, su ba dolaye ba ne, kuma idanunsu a bude yake .”
Cif Akin Oke, wanda ya fadi haka a cikin hira da wakilinmu ta waya a Ibadan. Ya ci gaba da cewa, “shekaru biyu da suka wuce idan aka ambaci sunan Buhari mutane da ke zaune a wannan sashe ba sa sauraro, amma a cikin watanni 6 da suka wuce sai wakokin ambaton sai Buhari! Sai Buhari! Sai Buhari! ake yi a ko’ina. Saboda haka mafi yawancin jama’a magoya bayan APC da sauran jama’a sun riga sun zartar da hukumcin kada kuri’unsu ga Janar Muhammadu Buhari ne a zabe mai zuwa. Babu wata farfaganda da za ta canza wa jama’a zaben abun da suke so.”
A ranar Asabar da ta wuce ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya kai wata ziyara garuruwan Oyo da Ogbomoso, a inda ya yi wata ganawa da Mai martaba Alaafin na Oyo Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi a fadarsa da ke garin Oyo. Daga bisani kuma ya zarce zuwa fadar Soun na Ogbomoso domin yin irin wannan ganawar ta sirri. Kafin nan a cikin makon jiya shugaban ya yi irin wannan ganawa da wadansu dattijan yarbawa da wadansu shugabannin al’ummomin Hausawa da Ibo da ke zaune a birnin Legas.