✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

John Mikel Obi ne ya fi kowane dan kwallo samun kudi a Najeriya

Yan kwallo uku da aka tabbatar a halin yanzu sun fi kowane ’yan kwallo samun kudi a Najeriya su ne, John Mikel Obi da yanzu…

Yan kwallo uku da aka tabbatar a halin yanzu sun fi kowane ’yan kwallo samun kudi a Najeriya su ne, John Mikel Obi da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Chelsea da ke Ingila da Obafemi Martins da ke wasa a kulob din Seatle Sounders na Amurka da kuma Yakubu Aiyegbeni da ke buga kwallo a Ingila.

Kamar yadda kafofin watsa labarai da dama suka tabbatar, dan kwallon Chelsea John Mikel Obi shi ne na daya a halin yanzu. Yana karbar albashin Dala dubu 120 kwatankwacin Naira miliyan 20 a duk mako baya ga wadansu alawus-alawus da dan kwallon ke karba ciki har da na fafatawa a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai wtaau UEFA Champions League da ba a lissafa da su ba.
Obi, mai kimanin shekara 25 an ruwaito ya mallaki rukunan gidaje (Mansions) a birnin Jos da Legas da kuma a Ladan da kudinsu ya kai Naira miliyan 800. Sannan an ruwaito yana da hannayen jari a kamfanoni masu yawa a ciki da wajen Najeriya.
A kwanakin baya ne aka ji dan kwallon yana cewa har yanzu ya rasa matar da zai aura duk kuwa da arzikin da Allah Ya yi masa.
Shi kuwa Obafemi Matrins an ruwaito ya mallaki manyan otel-otel a Italiya da gidaje a birnin Legas da aka kiyasta kudinsu sun kai Naira miliyan 500. Kwanan nan Martins ya kaddamar da gidauniyar tallafawa marasa galihu a Italiya inda ya bada tallafin Naira miliyan 400.
Yakubu Aiyegbeni kuma an tabbatar ya mallaki kadadori da suka hada da gidaje da ote-otel a Jihar Edo, Jiharsa ta asali da kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan 400. Shi ma dan kwallo ne da a halin yanzu ya mallaki hannayen jari a kamfanonin da ke ciki da wajen kasa.