Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Joe Biden, ya kirayi Shugaba Muhammadu Buhari da Sojin Kasa na Najeriya, da su daina amfani da karfin tsiya wajen dakile zanga-zangar masu nuna kin jinin rundunar tsaro ta SARS.
Kiran da Mista Biden ya yi na zuwa ne awanni kadan bayan da sojoji a ranar Talata suka bude wuta a kan matasa masu zanga-zanga a dandalin Lekki da ke birnin Legas.
- Babu hannuna a kisan masu zanga-zangar —Tinubu.
- Hilary Clinton ta gargadi Buhari a kan kashe masu zanga-zangar #EndSARS
Biden wanda shi ne dan takarar Shugabancin Amurka na Jam’iyyar Democrat ya ce, “Ina kira ga Shugaba Buhari da sojojin Najeriya da su dakatar da mummunar murkushe masu zanga-zanga a Najeriya, wanda tuni ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
“Zuciyata na nuna juyayi ga duk wadanda suka rasa wanda suke kauna a rikicin.”
“Dole ne Amurka ta goyi bayan ’yan Najeriya wadanda ke yin zanga-zangar lumana don sake fasalin ’yan sanda da neman kawo karshen cin hanci da rashawa a dimokuradiyyar su.”
“Ina karfafa gwiwa ga gwamnati da ta shiga tattaunawa tare da kungiyoyin farar hula don magance wadannan korafe-korafen da aka dade ana yi tare da yin aiki tare don samar da Najeriya mai adalci da hada kan jama’a”, in ji sanarwar da Mista Biden ya fitar.
Aminiya ta ruwaito cewa, tuni dai zanga-zangar ta rikide zuwa rikici tsakanin masu gudanar da ita da wasu da ake zargi ’yan daba ne a wasu manyan biranen kasar da suka hada da Kano, Benin, Legas da Abuja.