✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin sojin Pakistan ya yi hatsari, ya kashe dukkan mutanen cikinsa

Wannan ne karo na biyu da jirgin ka hatsari cikin wata biyu

Wani jirgin sojin kasan Pakistan ya yi hatsari yayin wani sintirin da yake cikin dare a lardin Balochistan, inda ya kashe dukkan mutum shidan da ke cikinsa, ciki har da wasu manyan jami’an sojin su biyu.

A cikin wata sanarwar da ta fitar da safiyar Litinin, Rundunar Sojin kasar ta ce jirgin mai saukar ungulu dai ya fado ne cikin daren Lahadi a garin Khost mai nisan kimanin kilomita 12 daga Quetta, babban birnin lardin na Balochistan.

“Wani jirgin sojin da ke kan aiki ya fado cikin dare. Mutum shida, cikinsu har da Janar din soja guda biyu sun yi shahada a hatsarin,” inji sanarwar.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan musabbabin hatsarin ba ko yanayin aikin da sojojin suke yi lokacin da suka gamu da iftila’in.

A cikin wani sako da ya wallafa da ya harshe Urdu a shafinsa na Twitter ranar Litinin, Firaministan kasar, Shehbaz Sharif ya yi wa mamatan da iyalansu addu’ar fatan Allah Ya jikansu.

Shi kuwa shugaban ’yan adawar kasar kuma tsohon Ministan Yada Labarai, Fawad Chaudry, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan lafiyar jiragen sojojin kasar don kauce wa sake aukuwar hakan a nan gaba.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake samun hatsarin jirgin a kasa da wata biyu, kodayake hukumomin kasar sun ce suna bincike a kai.

Ko a ranar daya ga watan Agustan da ya gabata sai da wani jirgin na sojoji ya yi hatsari a yankin Lasbela na Balochistan din, inda shi ma ya kashe mutum shida, ciki har da wani babban jami’in soji.