✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin sojan kasar Cuba ya yi hatsari, ya hallaka dukkan mutanen cikinsa

Wani jirgin sojan kasar Cuba ya yi hatsari tare da hallaka dukkan mutane biyar din dake cikinsa a gabashin kasar.

Wani jirgin sojan kasar Cuba ya yi hatsari tare da hallaka dukkan mutane biyar din dake cikinsa a gabashin kasar.

Rundunar sojan kasar ce ta tabbatar da faruwar hatsarin inda ta ce ya faru ne ranar Juma’a.

A cewar rundunar, hatsarin ya faru ne jim kadan bayan jirgin ya bar yankin gabashin Holguin a kan hanyarsa ta zuwa gundumar Guantanamo, kamar yadda wata takaitacciyar sanarwa daga rundunar sojan ta tabbatar.

Ya zuwa yanzu dai babu wani karin bayani kan musabbabin abinda ya haifar da hatsarin.

Amma tuni rundunar ta ce ta kaddamar da bincike domin gano musabbabinsa.