✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin saman sojoji ya hallaka ‘yan bindiga 20 a Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, sashen rundunar mai taken Operation Hadarin Daji, ya yi nasarar murkushe ‘yan bindiga 20 a wani wuri kusa da…

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, sashen rundunar mai taken Operation Hadarin Daji, ya yi nasarar murkushe ‘yan bindiga 20 a wani wuri kusa da yankin Munhaye a jihar Zamfara.

Kakakin Rundunar sojojin saman Najeriyar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ne da ya fitar cikin wata sanarwa da ya yi a yau Laraba, ya ce, an hallaka ‘yan bindigar ne a wani harin sama da rundunar ta kaddamar jiya Talata.

Ya bayyana cewa, an kaddamar da samamen ne bayan wasu sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu, cewa ‘yan bindigar suna tattaruwa ne a wannan wurin da nufin gudanar da wani taro.

Ya ci gaba da cewa, rundunar ta yi amfani da wani jirgin yakin Alpha Jet wajen farwa wurin da ‘yan bindigar suka taru; wanda yake da nisan Kilomita 15 daga kan iyakar Jihar Zamfarar da Jihar Katsina.

Ya ce, isar jirgin wannan yankin ke da wuya, sun hango ‘yan bindigar da yawansu ya kai 30 suna neman arcewa sa’annan kuma suna ta kokarin harbin jirgin. Amma dai jirgin yakin ya yi nasarar bude wuta kan ‘yan bindigar inda nan take ya hallaka 20 daga cikinsu.