Wasu hafsoshin soja sun rasu a wani hatsarin jirgin soja da ya ritsa da su a Jihar Kaduna a yammacin ranar Talata.
Majiya mai tushe ta ce matuka jirgin su biyu sun rasu ne a lokacin da suke samun horo a sansanin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke Kaduna.
- Yanzu Najeriya ce kasar da kungiyar IS ta fi kai wa hari a duniya —Rahoto
- Ba za mu yaki ’yan bindiga da jiragen Super Tucano ba sai 2023 —Gwamnati
“Abin takaici ne yadda muka rasa wasu jajirtattun hafsoshinmu biyu, Allah Ya jikan su,” a cewar majiyar mai tushe.
Mun yi kokarin samun karin bayani daga kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, saboda mun kasa samun shi a waya.
Hatsarin jirgin ya faru ne kimanin shekara guda bayan wani makamancinsa da ya ritsa wasu manyan hafsojin sojin kasa a watan Mayun 2021 a Jihar Kaduna.
Hatsarin na 2021 ya yi ajalin manyan hafsoshin sojin kasa 11, ciki har da Babban Hafsan Sojin Kasa, marigayi Manjo Janar Ibarhim Attahiru, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa halartar taron yaye kuratan sojoji a Zariya.