Mutane 17 sun bace yayin da aka ceto wasu biyu bayan da wani jirgin ruwan kamun kifi ya nitse da su a Tekun Barents dake kasar Rasha.
Kafafen watsa labaran kasar sun ruwaito cewar lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
- Gobara ta sake tashi a tashar jirgin ruwan Lebanon
- Hatsarin jirgin ruwa ya kashe mutum 10
- Sama da mutum 140 ake tsoron sun rasu a hadarin jirgin ruwan Kamaru da na Libya
- An sallami jagoran ’yan adawar Rasha, Alexei Navalny daga asibiti
Rahotanni sun ce jirgin ruwan mai lakabin ‘Onega’ ya nitse ne a kusa da tsibirin Novoya Zemlya dauke da mutane 19 a ciki.
Tuni dai rahotanni suka ce Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasar ta bazama domin ceto wanda suka nitse a ruwan.
Ma’aikatar ta danganta faruwar lamarin da yawaitar dusar kankara da jirgin ruwan ya tarar.
Yanzu haka dai ana ci gaba da kokarin ceto mutanen, sai dai an gaza tura jirgin sama saboda matsalar yanayi da ake ciki.