✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki —NRC 

Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya samu matsala sakamakon sauka daga titinsa da ya yi.

Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da dawowar aiki  jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wanda aka dakatar sakamakon hatsari da ya yi a tashar Kubwa a makon da ya gabata, ranar Juma’a 27 ga watan Janairu, 2023.

NRC a cikin wata sanarwa, Daraktan Ayyuka, Injiniya Niyi Ali, ya ce jirgin zai dawo aiki a ranar Talata 31 ga Janairu 2023.

Jadawalin jirgin da aka fitar ya nuna jirgin farko daga Kaduna zuwa Abuja zai tashi da karfe 7 na safe yayin da jirgin farko daga Abuja zuwa Kaduna zai tashi da karfe 10 na safe.

Jirgi na biyu daga Kaduna zai tashi da karfe 1:00 na rana, yayin da jirgin Abuja zuwa Kaduna zai tashi da karfe 4 na yamma.

Sai dai a ranar Laraba jirgin kasa daya ne zai tashi daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 7 na safe sai kuma wanda zai tashi daga Abuja zuwa Kaduna da misalin karfe 4 na yamma.

“Muna nadamar duk wata matsala da fasinjojinmu masu suka fuskanta sakamakon matsala da jirgi ya samu ya samu.”