Akalla mutum hudu ne suka rasu wasu da sama suka samu raunuka bayan wani jirgin kasan fasinja ya yi hatsari a Jihar Bihar ta kasar Indiya.
Rahotanni sun ce jirgin kasan dauke da fasinjoji zuwa birnin Delhi daga tashar Anand Vihar, taragansa 21 ne suka sauka daga layin dogo a daren Laraba.
A safiyar Alhamis wani babban jami’in sufurin jiragen kasa, Tarun Prakash, ya sanar cewa “ana ci gaba da aikin ceto amma mutum hudu sun mutu, wasu da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin kasan.”
Ministan sufurin jiragen kasa, Ashwini Vaishnaw ya jajanta wa wadanda hatsarin ya shafa, yana mai cewa an sauya wa fasinjojin jirgi domin karasa tafiyar tasu, amma mai yi magana kan mamatan ba.
Sai dai rahotanni sun ce an garazaya da wadanda suka samu rauni asibiti domin ba su kulawa.