Jirgin farko dauke da kayan hatsi ya bar Ukraine bayan ta kulla yarjejiya da Rasha domin barin ta fitar da kayan hatsin da suka makale zuwa kasashen duniya.
Jami’an gwanatin Turkiyya da Ukraine sun bayyana cewa jirgin ya tashi ne daga Tashar Jiragen Ruwa ta Odesa da ke Ukraine a safiyar Litinin.
- Ukraine ta kashe sojojin Rasha 100 a Kherson
- Ta’addanci: Daruruwan mutane sun tsere daga yankin Birnin-Gwari
Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya bayyana fara jigilar hatsin a matsayin “sauki ga al’ummar duniya” sannan ya yi kira ga Rasha da ta “cika bangarenta na yarjejeniyar” da kasashen biyu suka kulla.
Ofishin kula da aiwatar da yarjejeniyar Rasha da Ukraine da ke Istanbul ya ce jirgin na dauke da ton 26,000 na masara, kuma ana sa ran isarsa kasar Turkiyya a ranar Talata domin a bincike shi.
Ya bayyana ta shafinsa na Facebook cewa, “A yau, mu da kawayenmu mun dauki wani babban mataki na kawar da yunwa a fadin duniya.“
Rufe tashoshin jiragen Odesa
Tun a watan Fabrairu da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine ta tare tashoshin jiragen ruwan kasar, amma daga bisani suka rattaba hannu kan yarjejeniyar barin Ukraine ta ci gaba da jigilar kaya.
Ana fata ci gaba da jigilar kayan hatsin zai sassauta tsadar hatsi da kuma barazanar yunwa da duniya ke fuskanta.
Kubrakov ya ce, “Bude tashoshin jiragen ruwan zai samar da akalla Dala biliyan daya ga tattalin arziki da kuma karin daga ga bangaren noma a cikin shekara daya mai zuwa.”
A watan Yuli ne Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka yi nasarar ganin Rasha da Ukraine sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar fitar da hatsi daga Odesa, bayan shafe kusan wata biyu suna fadi-tashi.
Akwai yiwuwar sabunta yarjejeniyar ta wata hudu, idan kasashen biyu suka amince.
Karfin samar da hatsi da duniya
Tare tashoshin jiragen ruwan da Rasha ta yi wa Ukraine ya haifar ta tashin gwauron zabo da karancin hatsi a duniya, musamman ma kayan alkama da takin zamani da kuma man girki.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna a 2019 Ukraine ta samar da kashe 16 cikin 100 na masara da kuma kashdi 42 cikin 100 na man girkin sunflower a fadin duniya.
Yarjejeniyar Rasha da Ukraine
A karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, sun amince ba za a kai hari kan tashoshin jiragen ruwa ba, kuma jiragen sojin Ukraine za su yi wa jirage masu dakon kaya a wuraren da ke cikin hadari.
Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya kuma za su tantance jiragen domin tabbatar da ba sa dauke da makamai ko yin fasakwauri, kamar yadda Rasha ke zargi.
Tashoshin jiragen ruwa uku ne a Kudancin kasar Ukraine — Odesa da Chornomorsk da kuma Pivdenny – kuma hankali ya fi karkata zuwa kansu a game da batun.
Da farko dai yarjejeniyar ta fuskanci baranzana, kasa da awa 24 kafin sanya hannu a kanta, inda Rasha ta kai hari a tashar jiragen ruwa ta Odesa.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce harin ya nuna Rasha ba ta shirin cika alkawuran da ta dauka.
Amm Rasha ta ce ta kai harin ne a kan wani jirgin sojin ruwa da ke tashar, ta kuma kekashe kasa cewa harin bai shafi yarjejeniyar ba.