✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgi mai saukar angulu ya yi hatsari a Legas

Ya yi hatsarin ne a kusa da filin jirgin saman Legas

Wani jirgin sama mai saukar angulu da ba a kai ga tantancewa ba ya yi hatsari a kan wani gini da ke unguwar Ikeja a Jihar Legas.

Jirgin dai ya kama da wuta ne a kusa da filin jirgin sama na Murtala Muhammed, wajen da yake shirin sauka.

Kodayake an samu nasarar ceto mutum biyu da aka yi ittifakin direbobin jiragen ne a raye, amma babu tabbacin adadin yawan fasinjojin da ke cikin jirgin.

Tuni dai jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) suka isa wajen inda suke koarin aikin ceto.