✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindiga a Kaduna

Jinrage sun yi luguden wuta kan ’yan bindiga a inda suke boye shanun sata.

Jiragen sama sun yi ruwan wuta a kan sansanin ’yan bindiga masu satar shanu a Jihar Kaduna inda suka hallaka da dama daga cikinsu.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan da yawa a Karamar Hukumar Giwa a yayin sintirin da jiragen suka gudanar a Kananan Hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi da kuma Chikun.

Ya ce jiragen sun gano wasu matattaran ’yan bindiga ciken da garken shanun sata a yankin Yadi a Karamar Hukumar Giwa, inda nan take  suka bude musu wuta.

Ya ce yankunan aka gudanar da sintirin sun hada da Kajuru, Kachia, Zonkwa, Manchok, Zangon Kataf da sauransu.

’Yan bindiga sun hallaka a Kaduna 

Sai dai kuma ya ce ’yan bindiga sun kashe mutane shida a wasu sabbin hare-hare a Kananan Hukumomin Igabi da Kauru a Jihar Kaduna.

Aruwan ya ce an kai hare-haren ne a Kananan Hukumomin Igabi da Kauru a ranar Talata inda aka kuma jikkata wasu da dama.

Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tare hanyar Birnin Yero zuwa Tami inda suka kashe wani mutum suka kuma jikkata wani wanda yanzu ake jinyarsa.

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu-biyu a kauyen Gwada da Ungwan Kure duk a karamar hukumar Igabi.

“Sun kuma kai hari a Amawan Dadi Rugan Jauru a Karamar Hukumar Kauru inda suka harbi wani mutum da aka fi sani da ‘Likita’,” inji Aruwan.