✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen Yaki Sun Kashe Manyan Kwamandojin ISWAP A Tafkin Chadi

Jiragen yakin sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin  ISWAP uku a maboyar kungiyar a yankin Tafkin Chadi.

Jiragen yakin sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin  ISWAP uku a maboyar kungiyar a yankin Tafkin Chadi.

Wata majiyar tsaron ta tabbatar da mutuwar manyan kwamandojin kungiyar uku a harin, da suka hada da Mohammed Balke, Malam Ciroma da Bashir Sniper.

Mutanen uku sun mutu ne a lokacin da jirgin ya jefa bam a maboyarsu da ke Jibilaram.

Mohammed Balke shi ne shugaban gidan yari kuma mai kula da masu garkuwa da mutane na ISWAP;  Malam Ciroma shi ne mataimakinsa na biyu; Bashir Sniper kuma shi ne kwamandan kungiyar da ke kula da hanyoyin shiga dukkan tsibiran da ke karkashinta.

Wata majiyar tsaro ta ce a ranar Talatar jiragen yakin sojin Najeriya suka yi luguden bama-bamai a tsibiran Jibillaram da Rino da Kangarwa, wadanda sansanoni ne na kungiyar ISWAP inda suka kashe mayakan da dama tare da yi wa kungiyar ta’addancin mummunar barna.

“Gaskiya ne jiragen Najeriya sun yi luguden wuta a Jibillaram da Rino a yankin Marte da Kangarwa a yankin Kukawa kwana biyu da suka wuce,” kamar yadda wata majiya ta leken asiri ta shaida wa Aminiya.

Ta ci gaba da cewa, “Ana ci gaba da tantance girmar barnar da aka yi wa bata-garin kuma a hankali ana samun bayanai.”