Fadar Shugaban Kasa ta ce kwararan dalilan sun nuna cewa jiragen sama na yi wa ’yan bindgia dakon makamai.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana wa Aminiya haka ne yayin bayani kan haramta shawagin jirage a Jihar Zamfara da Gawmanti Tarayya ta yi.
- Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindiga a Kaduna
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
- Buhari ya haramta tashi da saukar jirage a Zamfara
Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya kuma haramta ayyukan hakar zinare a Zamfara ce saboda an gano cewa miyagu a jihar na yin musayar makamai da zinarin da ake haka ba bisa ka’ida ba.
“A Zamfara akwai kwakkwaran zargi cewa helikwaftoci na kai wa ’yan bindiga makamai da kuma yin fasakwaurin zinarin daga Najeriya, shi ya sa kasar ke ta asara a bangaren hakar ma’adanai.
“Kasuwaancin zinaren Najeriya na da girma saosai kuma gwamnati so take ta jefi tsuntsu da dutse daya; kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da kuma fasakwaurin zinare da ke yi wa tattalin arzikin kasar nan kutungwila,” inji shi.
Garba Shehu ya bayyana cewa akwai wata babbar kasuwar hadahadar zinare a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ake kira Kasuwar Zinarin Najeriya wato “Nigerian Gold Market” a Turance.
Tuni dai Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin na haramta shawagin jiragen sama a Jihar tasa.
Matawalle ya bayyana mamakinsa kan yadda matakin zai yi wani tasiri wurin yaki da ayyukan ’yan bindiga da suka hana ruwa gudu a jihar.