Jirgin kasa ya kasance wani inji mai tafiya a kan kasa, a karkashin kasa ko a saman benaye a wasu kasashe. Har yau Indiya ta dogara da tsarin jiragen kasa saboda yawan talakawa, wadanda kan dogara da wannan hanyar don sauki duk nisan wuri, duk da cewa akan cunkushe ko a bayan amalanken jiragen kasa. Amma abin hawan hawa ne, akwai amalanken sarakuna da ta anguna tare da na leburori.
A nan Afirka akwai kasashe kamar Masar da Afirka ta Kudu, inda suke da jiragen kasa da na karkashin kasa don wutar lantarki ta tsaya, yayin da wasu kasashen da suka ci gaba kamar Malaysia da Singapore da China da uwa uba Indiyar, har a jikin dogayen benaye ko gadojin da za su tsallake mutane daga wani sashin garin zuwa wani sashi.
A duk ababen da ake amfani da su wajen sufuri a kasa da ruwa da iska (sama). Tabbas kowa ya san kasa a shimfide take don mu taka, mu gina gidaje mu rayu. Amma baiwa da kirkira ta sa aka gano cewa za a iya tafiya, doguwar tafiya mai nisa a kan ruwa da iska.
Duk da haka dole sai an bi ta kasa kafin a kai ga inda za a je ko aje kayan, wato koda ta sama aka kai mutum sai ya shiga mota ko ya hau babur kafin ya je kofar gidansu, domin jirgin saman ba zai kawo ka kofar gida ba.
Wani abin mamaki game da yadda ake tafiyar da sufuri a Najeriya, shi ne yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi kokarin kafa jiragen kasa a kasar nan, amma hakarsu ta kasa cimma ruwa. Kullum sai a gayyato kasashe don cimma wannan buri, yayin da muke fata wannan gwamnatin za ta tabbatar da wannan kuduri.
Jirgin kasa yana da muhimmancin gaske wajen bunkasa kasa, domin da jiragen kasa ne aka kawo kaya, masu nauyi tare da daukar sanadarai da dabbobi cikin kulawa da hanya mai sauki, domin ba cinkoso a hanyarsa, kuma a zamanance jiragen masu gudu ne fiye da motoci sannan ga kayatarwa wajen gamsarwa da jin dadi da nishadi. Dadin dadawa ga arha kowa zai iya hawa jirgin kasa.
Lokaci ya yi da za a gyara jiragen kasa, musamman ganin yadda titunan kasar nan suka zama wasu tarkunan mutuwa. Sannan jirgin kasa hanya ne na karbar haraji cikin ruwan sanyi. Tare da ba da tsaro ga masu amfani da shi, don da wuya ka ji ya kife ko sun yi karo.
Bugu da kari bai kamata kowane Gwamna ya sa burin sai ya kafa filin jirgin sama a babban birnin jiharsa ba. Wasu jihohin suna kusa, wasu jihohin kuma idan ba daurin aure ko mutuwa ba, ba wanda yake kai musu ziyara. Sannan ba kamfanoni a jihohin, kuma a duba mene ne muhimmancin hakan, kuma shin hakan zai kawo baki jihar?
Idan Buhari ya tabbatar da jiragen kasa sun dawo, shi ne kokarin da zai yi wa talakawa. A zahiri mutane nawa ke iya hawa jirgi daga Kano zuwa Legas? Bayan kudin sufurin jirgin saman ya fi kudin wata, fiye da rabin ’yan Najeriya! Wai ma mutane nawa ne suke, ko suka taba hawa jirgin sama a kasar nan, don yadda al’amarin ke da tsada da hadari.
Talakawa za su mori jirgin kasa, talaka ne ke shan wahalar idan man fetur ya kara tsada, bisa ga haka aka yi yunkurin farfado da marigayin nan Nigerian Airways, wato kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya. Gara dai a yi abin da zai yiwu, wato a gyara jiragen kasa. Saboda haka ina kara kira ga gwamnati, musamman ga Ministan Sufuri, Rotimi Amechi ya yi hobbasa don tabbatar da zamanantar da jiragen kasa a kasar nan. Ina fata jirgin kasa zai ratsa kauyenmu.
Buhari Daure +2347035986444, Muryar Talaka kofar kaura, Katsina.
Jiragen kasa za su ratsa kauyenku
Jirgin kasa ya kasance wani inji mai tafiya a kan kasa, a karkashin kasa ko a saman benaye a wasu kasashe. Har yau Indiya ta…