Sanya hannu a kan kudirin dokar da ta amince a yi jinya ga masu raunin harbin bindiga ba tare da rahoton ’yan sanda ba da Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya yi, abin maraba ne ga batun da ake ta kokawa a kai shekara da shekaru, lamarin da kuma yake jawo asarar rayuka tare da fusata dangin wadanda lamarin ya shafa.
Sanya hannu a kudirin dokar mai taken: Dokar Tilasta Yin Jinya da Kula da Wadanda Suke da Harbin Bindiga ta Shekarar 2017, ta sa yanzu ma’aikatan kiwon lafiya suna da ’yancin su yi jinya ga mai raunin harbin bindiga ba tare da jiran rahoton ’yan sanda ba.
Babban Mai tallafa wa Shugaban kasa kan Harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Ita Enang y ace dokar harbin bindigar ta bayyana cewa wajibi ne a karba tare da yin cikakkiyar jinya ga duk mutumin da yake dauke da harbin bindiga a kowane asibiti na Najeriya ya allay a ajiye kudi a asibitin ko bai ajiye ba.
“Kuma babu dama a tozarta mutumin da ke tare da harbin bindiga ba, ko a ki yi masa jinya ko a musguna masa daga wani mutum ko wata hukuma, ciki har da ’yan sanda da sauran jami’an hukumomin tsaro,” inji shi.
Shekaru da dama mutanen da suka samu raunin harbin bindiga da aka kai su asibiti galibi akan ki yi musu jinya har sai an sanya ’yan sanda a ciki. Tunanin da ake yi shi ne duk wanda ya je asibiti dauke da harbin bindiga kila dan fashi da makami ne ko mai wani mugun laifi. Wannan mummunan tunani ne, kuma saboda akwai miyagun masu dauke da makami a cikin jama’a, tana iya yiwuwa wancan mutumin da yake da harbin bindiga ya fada hannunsu ne, ba ya daga cikin miyagun. Kuma koda wanda ke dauki da harbin mai mugun laifi ne, zai fi kyau a fara yi masa jinya lura da yanayin aikin gaggawa da ake bukata ga raunin harbin bindiga, sannan sai a sanar da ’yan sanda su zo a daidai lokacin da ake cikin jinyar. Ta wannan hanya zai iya bayar da bayanai masu amfani da za su iya ceto jama’a, maimakon a kyale shi ya mutu, wanda hakan zai dada tabarbara lamarin. Masu aikata miyagun laifuffuka da dama sun mutu ta wannan hanya, kuma hakan ya sa sun shiga kabari tare da muhimman bayanai.
Sanya hannu a kan kudirin dokar ya fi zama mai alfanu a yanzu saboda irin dimbin nau’o’in miyagun ayyuka kuma watsuwar kananan bindigogi a kasar nan babu wanda rayuwarsa ta tsira, domin kowa yana iya haduwa da harbin bindiga. A wurin da satar mutane ana garkuwa da su da fada a tsakanin kungiyoyin asiri da fashi da makami da ayyukan ’yan bindiga da sauransu suke cin kasuwa, zai zamo abin takaici a ce asibitoci sun ki karbar wadanda aka harba da bindiga.
Sanya hannu a kudirin dokar ba yana nufin kawo karshen lamarin ba ne. Akwai bukatar a wayar da kan jama’a sosai ta rediyo da talabijin domin a mayar da martani kan tsohon tsarin nan na ‘In babu rahoton ’yan sanda babu jinya’ da asibitocin ke yi wanda ya riga ya samu gurbin zama a zukatan jama’a.
Batun ajiye kudi kafin a fara jinya abu ne da ya zama ruwan dare a asibitocinmu komai munin rauni, abu ne da ya kamata a magance shi a wannan bangare kamar yadda Enang ya nanata.
Don haka, asibitoci ba su da wani uzirin cewa ba a ajiye kudi ba, don haka su kyale mai raunin ya mutu.
Gaskiyar magana ma ita ce mutanen da suka kai shi asibitin ba lallai ba ne su san shi. Kuma koda dangi ne suka kai mai harbin bindigar asibitin, a wannan yanayi na gaggawa da ceto rayuwarsa ce mafi muhimmanci, bai kamata a damu da batun kawo kudi a wannan lokaci ba. Kamata ya yi su nemi hakan bayan mai jinyar ya dawo cikin hayyacinsa.
Don haka muna kira ga shugabannin asibitoci da ma’aikatan kiwon lafiya su yi aiki da wannan doka kuma su fadakar da sassan da ke kula da raunika na asibitocinsu inda ake kai masu raunin harbin bindiga da sauran wadanda za su nemi a biya kudi.
Duk wani batun kudi a bari a warware shi daga baya. Ma’aikatar Lafiya da Sassan Lafiya na kananan Hukumomi, wajibi ne su bullo da hanyar da za a ilimantar da ma’aikatan lafiya kan wannan doka.
Wajibi ne kuma gwamnatin ta tabbatar da asibitoci suna bin wannan doka sau-da-kafa ta hanyar karfafa wa jama’a gwiwa suna kan rahoto ga hukumomi kan duk asibitin da ya ki karbar mai rauni harbin bindiga. Kuma akwai bukatar a hukunta duk asibitin da aka samu yak eta wannan doka. Wannan wani lamari ne da ya shafi rayuwa da mutuwa.