✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin Arewa maso Gabas sun goyi bayan kasancewar kasar nan a dunkule

Jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Bauchi da Borno da Gombe da kuma Yobe sun goyi bayan kasar nan ta ci gaba da…

Jihohin Arewa maso Gabas da suka hada da Bauchi da Borno da Gombe da kuma Yobe sun goyi bayan kasar nan ta ci gaba da zama a matsayin dunkulalliyar kasa tare da ra’ayoyi mabambanta.

Da yake jawabi a taron da Jam’iyyar APC ta kasa ta kira don jin ra’ayin al’ummar Shiyyar Arewa maso Gabas a Bauchi, Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce mafi yawan al’ummar kasar nan sun yi imani da kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Gwamnan wanda Mataimakinsa Nuhu Gidado ya wakilce shi ya ce duk wanda bai amince da tsarin mulkin kasar nan ba kamata ya yi ya tura korafinsa ta hanyar da ta dace, sai ya bukaci a bai wa jihohi da kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu ta fannin bunkasa aikin gona.

Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Geidam wanda Babban Sakataren Ayyuka na Musamman na Gidan Gwamnatin Jihar, Alhaji Lawal Usman Hassan ya wakilta ya nanata goyon bayansu kan hadin kan kasar nan domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Shugaban Majalisar Malamai ta kasa reshen Jihar Bauchi Ustaz dan’azumi Musa Tafawa balewa da Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa reshen Jihar Bauchi, Rabaran Ezikiel Abasu sun yi kira a dawo da tsarin mulki na Firayi Minista, tsarin da suka ce ba ya da tsada in aka kwatanta shi da tsarin mulkin da ake amfani da shi a yanzu. Shugabannin addinin sun ce ba sa goyon raba kasar nan ta yadda za a bai wa jihohi damar cin gashin kansu su zama kowace jiha na da sojoji da ’yan sanda. Kuma sun nuna damuwa kan yadda jama’a ke shan wahala a jihohin, inda suka ce idan an kawar da cin hanci da rashawa aka bai wa kowa ’yancin yin abin da ya dace da shi za a zauna lafiya. Sun ce wadannan kiraye-kiraye sun taso ne saboda yadda ake danne hakkin mutane.

Shugaban kungiyar Kwadago ta Jihar Bauchi, Kwamred Hashimu Gital ya nuna goyon bayansu kan bai wa kananan hukumomi ’yancin gashin kansu. A jawabinsa Shugaban Kwamitin Jam’iyyar APC da ta shirya taron na Arewa maso Gabas, Farfesa Osahemin Osinba ya nanata niyyar jam’iyyar ta tabbatar da dorewar dimokuradiyya a kasar nan.  Farfesa Osinba ya ce jam’iyyar ta himmatu wajen raba arzikin kasar nan ta hanyar jihohi da kuma kananan hukumomi, kuma ya ce tsarin jam’iyyar ce su gana da a’lummar kasar nan domin samun maslaha.