✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jihar Sokoto ‘ta warke daga coronavirus’

An sallami ragowar mutum biyar da suka rage masu cutar coronavirus a jihar Sokoto. Warkewar mutanen biyar ya kara yawan wadanda suka warke daga cutar…

An sallami ragowar mutum biyar da suka rage masu cutar coronavirus a jihar Sokoto.

Warkewar mutanen biyar ya kara yawan wadanda suka warke daga cutar a jihar zuwa 102.

Mutum 116 ne suka harbu da annobar coronavirus a jihar, amma 14 daga cikinsu sun rasu.

A ranar Alhamis ne Kwamishinan Lafiya na Jihar Sokoto Dokta Ali Inname ya ce yanzu babu sauran mai cutar a jihar.

Sai dai Dokta Inname ya ce, “hakan ba ya kore yiwuwar sake bullar cutar ta COVID-19 a jihar.

“Za mu ci gaba da gwajinta, idan aka samu mai ita za mu killace shi a kula da lafiyarsa.”

Ya kuma jaddada kira ga jama’a da su daina kyamar wadanda suka warke daga annobar.

Ya ce kamuwa da cutar ba mutuwa ba ce kuma mutum na iya harbuwa da ita, ya warke bai ma sani ba.