✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Kano ta farfaxo da gasar KASHIGA

Hukumar Kula da Harkokin Wasanni ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya tsaf don  farfaxo da wasannin da ta saba gudanarwa a tsakanin manyan…

Hukumar Kula da Harkokin Wasanni ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya tsaf don  farfaxo da wasannin da ta saba gudanarwa a tsakanin manyan makarantun da ke jihar da nufin qulla zumunci a tsakanin xaliban jihar.

Aminiya ta rawaito cewa shi dai wannan wasa da ake yi wa take da KASHIGA an kwashe tsawon shekaru 20 rabon da a gudaar da shi a jihar.

Tuni dai Shugaban Hukumar Wasannin ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima da ’yan tawagarsa suka kai ziyarar tuntuva ga manyan makarantun  don fara wasannin a ranar 27 ga watan da muke ciki inda za a fara da wsan qwallaon qafa.

Makarantun da ake sa ran za su shiga gasar wasannin sun haxa da Jami’ar Bayero da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da Jami’ar North West da Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da Kwalejin Koyon Harkokin Shari’a ta Malam Aminu Kano da Kwalejin Fasaha ta Jihar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano da Makarantar Koyon Aikin Jinya ta Kano da ta Madobi da Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a.

Har ila yau Aminiya ta rawaito za a gudanar da wasannin ne a Jami’ar Bayero da Kwalejin Horor da Ma’aikatan Shigi da Fice ta Qasa da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano da kuma filin wasa na Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi.