Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da Kudurin Dokar ’Yancin Yara wanda aka yi wa kwaskwarima a shekara ta 2010.
Majalisar ta ce kudurin, wanda kowanne sashe nasa a yanzu ya dace da matsayin Shari’ar Musulunci an yi masa kwaskwarima ne bayan Gwamnatin Tarayya ta zartar da shi, kuma tuni suka mika shi ga zauren Majalisar Dokokin Jihar domin ya zama doka.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar ya ce an amince da kudurin ne yayin taron Majalisar Zartarwar da ya gudana a Fadar Gwamnatin jihar.
A cewarsa, “Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauki matakin ne saboda yadda ta damu matuka da kare hakkin yara, bayan ta amince da ilimi kyauta kuma dole ga dukkan yara a fadin jihar.”
Kwamishinan ya kara da cewa da zarar kudurin ya zama doka, zai taimaka wajen kare kananan yara daga duk wani nau’i na cin zarafi daga al’umma.
Ya ce tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta amince da kudurin a 2003, jihar Kano ta shiga fadi-tashi wajen aiki da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da malaman addini, ’yan boko da kungoyoyi masu zaman kansu wajen ganin an daidaita shi yadda zai dace da jihar.
Sai dai ya ce ko bayan yi wa kudurin kwaskwarima, an kasa zartar da shi a matsayin doka saboda jan-kafar da gwamnatocin baya suka yi.
A shekarun baya dai kudurin ya janyo cece-kuce sosai a Najeriya musamman a jihar Kano wadda mutane da dama ke ganin ya saba da al’adu da addinan mutanenta.