✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a rika dandake masu fyade a Jihar Kaduna

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar dandake masu aikata fyade a jihar

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar zartar da hukuncin dandaka ga masu aikata fyade a jihar.

Majalisar ta sanar cewa babban zaurenta ya amince da sabuwar dokar ce a lokacin zmaanta na ranar Laraba 9 ga watan Satumba, 2020.

“Kudurin gyaran Dokar Penal Court mai lamba 5 na shekarar 2017 ya zama doka jiya 9 ga watan Satumba, 2020.

“Dokar ta sanya a yi cikakken dandaka ga masu fyade a jihar”, kamar yadda Majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter.